Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, sun kama wasu mutane uku da ake zargi da yi wa ‘yan’tadda aikin masinja ta ha hanyar kai musu kuɗaɗen fansa da sauran kayayyaki, sannan sojojin sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a wasu ayyuka daban-daban a Ƙaramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.
A cewar kwamandan rundunar, ayyukan sun gudana ne a ranakun 24 da 25 ga Satumba, 2026.
A ranar 24 ga Satumba, dakarun sashe na 2 sun tare wasu mutane uku da ke tafiya a kan babur a Faskari. Binciken farko ya nuna cewa mutanen na ɗauke da naira miliyan 2.7, waɗanda ake zargin kuɗin fansa ne, tare da wayoyin hannu guda uku, domin kai su ga wani babban ɗanta’adda ta hannun wasu masu shiga tsakani a yankin.
Sojojin sun tsare mutanen tare da kayayyakin da aka ƙwato daga wurinsu domin ci gaba da bincike.
A washegari, dakarun da suka samu bayanan sirri kan motsin ’yanta’adda a yankin sun shirya kwanton-ɓauna tare da fafatawa da ‘yanta’addan, lamarin da ya tilasta musu tserewa. Binciken da aka gudanar daga bisani ya kai ga kwato bindigar AK-47 guda ɗaya, harsasai 30 da babur guda ɗaya.
A wani aiki na daban a wannan rana, dakarun da ke gudanar da sintiri na yau da kullum sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka ƙunshi maza 12 da mata biyu.
Rundunar sojin ta ce binciken farko ya nuna cewa an yi garkuwa da mutanen ne a ƙauyukan Anguwan Miko da Tafoki da ke Faskari. An ruwaito cewa ’yanta’addan sun bar mutanen ne bayan da suka hango dakarun sojin na tunkararsu.
Daga bisani an miƙa mutanen da aka ceto ga hukumomin Ƙaramar Hukumar Faskari domin ɗaukar matakan da suka dace.
Kwamandan rundunar ya ce ayyukan sun nuna ƙudurin Operation Fansan Yamma na kare fararen-hula, ceto mutanen da ake tsare da su da kuma takaita ayyukan ’yanta’adda da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a duk faɗin yankin da rundunar ke gudanar da ayyukanta.
Ya kuma yaba wa dakarun bisa taka-tsantsan da gaggawar mayar da martani, tare da kira ga mazauna yankin da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci kan duk wani motsi ko ayyuka waɗanda ake da shakku ko zargi a kansu a cikin al’ummominsu.


















