| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
FIFA ta musanta iƙirarin Maroko na 'karɓar baƙuncin' wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 2030
FIFA ta sanar da kafafan watsa labarai cewa za a cim ma matsaya kan wasan ƙarshe "nan gaba."
FIFA ta musanta iƙirarin Maroko na 'karɓar baƙuncin' wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 2030
Maroko za ta karɓi baƙuncin gasar ta shekarar 2030 tare da Sifaniya da Portugal.

FIFA ta mayar da martani ga iƙirarin da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Maroko ya yi cewa ƙasarsa za ta karɓi baƙuncin wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2030, tana mai cewa ba a yanke shawara ba tukunna game da batun.

Maroko za ta karɓi baƙuncin gasar ta shekarar 2030 tare da Sinafiya da Portugal. Wannan shi ne karo biyu da wata ƙasa ta Afirka za ta karɓi baƙuncin wasannin Gasar kofin Duniya, bayan Afirka ta Kudu ta karɓi baƙuncin gasar a shekarar 2010.

Fouzi Lekjaa, shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Maroko, ya bayyana ga waɗanda suka taru a wani taron siyasa ranar Alhamis cewa ƙasarsu ta sami damar karɓar baƙuncin wasan ƙarshe na gasar, in ji rahotanni.

"Birnin Benslimane zai karɓi baƙuncin wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya. Ka ƙi shi ko ka so shi, kuma idan kowa na son magana game da wannan, bari su yi magana," kamar yadda Lekjaa ya bayyana, bisa tafintar kamfanin dillancin labaran The Associated Press. "Birnin shi ne Benslimane, filin wasan Hassan II shi ne filin wasan, kuma ina fatan cewa Maroko za ta kasance cikin masu buga wasan."

FIFA ta sanar da wasu kafafan watsa labarai ranar Alhamis cewa za a cim ma matsaya kan ƙasar da za ta karɓi baƙuncin wasan ƙarshen "sannu a hankali."

Filin wasan da ake magana a kansa, wanda a hukumance ana ce masa Filin Wasan Sarki Hassan II, ana kan shirin gina shi kusa da birnin Casablanca kuma zai iya ɗaukar mutum 115,000.

Daga farko dai FIFA ta musanta rahotannin a kafafan watsa labaran Birtaniya cewa shugabanta, Gianni Infantino, ya yi wa Maroko alƙawarin wasan ƙarshe don goyon bayan siyasa yayin da yake neman sake takara a shekara mai zuwa.