Dakarun da ke kai farmakan HADIN KAI sun kama wani dan kasar Sudan da ake zargi da zama ɗanta’adda daga kasar waje, tare da wata mace ‘yan kasar Ghana da ta ce ba ta da takardun zama a yankin Askira/Uba da ke jihar Bornon Nijeriya.
Sojoji sun bayyana cewa, dakarun Bataliya ta 115 da Sashe na 4 na Farmakin HADIN KAI ne suka yi kamen, a yayin wani farmakin leken asiri da aka gudanar da misalin karfe 11:48 na ranar 19 ga Yuli.
Jami’an sojin sun bayyana sunan mutum na farko da Musa Fashir, mai shekaru 32 dan kasar Sudan.
Sun ce bayanan farko na leken asiri sun bayyana akwai yiwuwar yana da alaka da kungiyoyin ta’adda da ke Arewa Maso-Gabas, wanda ke kawo damuwa game da ‘yan kasar waje da ke da hannu a ayyukan ta’addanci a yankin.
Jami’an sojoji sun kuma kama Mary Florence mai shekaru 36, wadda ta sanar da masu bincike cewa ita ‘yar ci rani ce daga Ghana kuma ba ta da takardun zama.
Sojojin sun ce mahukunta na gudanar da bincike kan me ya kai ta wannan yankin, da kuma tabbatar da gaskiyar abin da ta fadi.
Ana ci gaba da tsare mutanen biyu a hannun jami’an tsaro, inda ake musu tambayoyi don tabbatar da su waye su, gano ayyukan da suke yi, da kuma gano ko suna da alaka da ‘yan ta’addar da ke yankin.
Ofishin kula da Farmakan HADIN KAI ya bayyana cewa kama mutanen na bayyana kwarewar ayyukansu na leken asiri da ke da manufar kawar da shigar mayakan waje yankin, da habaka tsaro a yankin arewa maso-gabashin Nijeriya.
Dakarun sojin sun kuma roki jama’a da su ci gaba da ba wa jami’an tsaro hadin kai da bayar da bayanai na gaskiya kuma a kan lokaci, inda suka ce hadin kan jama’ar na da matukar muhimmanci wajen dawo da zaman lafiya a yankin.



















