Masu kaɗa ƙuri’u a tsibirin na Sao Tome and Principe, wadda ake yi wa kallon abin koyi na dimokuraɗiyya a Afirka, suna kaɗa ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasa ranar Lahadi.
Shugaba mai ci Carlos Vila Nova yana fuskantar abokin hamayya na jam’iyya Nito Viegas D'Abreu, wani ɗanmajalisa mai ci da ke da goyon bayan tsohon Firaminista Patrice Trovoada, tare da ‘yantakara biyu masu zaman kansu.
Ƙasar, wadda Portugal ta yi wa mulkin mallaka a yankin tekun Guinea, ƙasa ce ta tsibiri mai mutane 200,000 wadda tarihinta ke cike da yunƙurin juyin mulki ciki har da wani yunƙurin kifar da gwamnati da rundunar sojin ƙasar ta daƙile nan-take a shekarar 2022.
Shugaban ƙasar na da muƙamin da ba shi da iko sosai, inda yake wakilta da kuma shelar dokoki yayin da yawancin ikon gwamnati ke hannun Firaminista.
Vila Nova, mai shekra 66, wanda aka zaɓa a matsayin shugaban ƙasa ne a shekarar 2021 da goyin bayan jam’iyyarsa ta ADI, yana bayyana kansa a matsayin mai tabbatar da "lumanar siyasa ta ƙasar".
Ya fuskanci suka game da korar tsohon firayiminista Trovoada a watan Janirun 2025, wani matakin da aka tabbatar da cewa ya saɓa wa tsarin mulki bayan shekara ɗaya .
Wurin yawon buɗe ido
Trovoada, wanda a yanzu shi ne shugaban ADI kuma yake neman ya sake samun muƙamin firayiminista a zaɓen ‘yanmajalisu a wannan watan Satumban, ya nuna goyon bayansa ga abokin hamayyar Vila Nova, Viegas D'Abreu.
Viegas D'Abreu, mai shekara 43, yana gabatar da kansa a matsayin wani wakilin waɗanda aka haifa bayan ƙasar ta samu ‘yancin kai a shekarar 1975.
Sao Tome and Principe na samun kuɗaɗen shiga ne daga noma musamman samar da koko da kofi da borkono.
Yanayin ƙasar na musamman ya sa masu yawon buɗa ido na zuwa ƙasar, musamman attajirai.
Manyan kamfanonin mai sun karɓi lasisin tonon mai da gas daga bakin tekun ƙasar cikin ‘yan kwanakin nan.
Duk da haka ƙasar na tsibiri ya kasance mai dogaro sosai kan tallafi daga ƙetare, inda da yawa daga cikin mutanenta ke rayuwa cikin talauci.






















