Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce yarjejeniyar tsaron haɗin gwiwa ta Makka da Pakistan da Saudiyya ba ta shafi Iran, Isra'ila ko wata ƙasa ba, yana mai jaddada cewa yarjejeniyar an yi ta ne don ƙarfafa tsaron yankin, hana rikita yankin da kuma samar da kwanciyar hankali.
Da yake magana a wata hira da mujallar Newsweek, Erdogan ya yi watsi da shawarwarin da aka bayar cewa ya kamata a ɗauki yarjejeniyar a matsayin ƙawance da nufin ƙalubalantar Iran ko Isra'ila ba tare da la'akari da garantin bayar da tsaro daga Amurka ba.
"Ba zai zama daidai ba a ɗauki Yarjejeniyar Tsaron Haɗin Gwiwa ta Makka a matsayin ƙawance da aka kafa don kalubalantar Iran, Isra'ila, ko wata ƙasa. Wannan yarjejeniyar tana nuna alhakin da muke da shi na gina makoma mai aminci, zaman lafiya, da wadata," in ji Erdogan.
Shugaban Turkiyya ya ce Ankara ta daɗe tana fafutukar ganin ƙasashen yankin sun ɗauki nauyin warware matsalolin da suka shafi yankin.
"Muna son ƙarfafa tsaronmu, ƙarfafa hana rikita yankin, da kuma ƙarfafa kwanciyar hankali mai ɗorewa a duk faɗin yankinmu," in ji shi.
Ya ce irin matakin da za a dauka a matsayin martani zai dogara ne kan bukatar kasar da aka kai wa harin.
"Wannan tallafi na iya haɗawa da bayanan sirri, kayan aiki da dabaru, ko kuma harsasai da makamai; yayin da kuma za a iya la'akari da samar da ƙarin tallafin soji mai zurfi dangane da girman barazanar," in ji Erdogan.
Ya ƙara da cewa hukumomin siyasa da na soji masu ruwa da tsaki ne za su tantance yadda za a aiwatar da irin waɗannan matakai, tare da gargadin kada a yi zaton cewa yarjejeniyar za ta haifar da shiga tsakani kai tsaye ta sojin Turkiyya idan aka kai hari.
"Saboda haka, ba zai dace a kudirci matakan soji na kai tsaye tun da wuri ba saboda duk wani lamari da ka iya faruwa a Iraki, Yemen, ko wani wuri daban," in ji shi.
Turkiyya za ta iya mu’amala da dukka bangarori
"Tun daga yakin Rasha da Ukraine zuwa tashin hankali a Gabas ta Tsakiya, Turkiyya kasa ce da ke da ikon shiga tsakani da dukkan bangarorin da ke rikici da daukar matakin zaman lafiya," in ji shi.
Da yake magana kan dangantakar da ke tsakaninsu da Isra'ila, Erdoğan ya soki abin da ya bayyana a matsayin wani labari da ke fitowa yana nuna Turkiyya a matsayin barazana.
"An kirkiri wani labari mara tushe kwanan nan a Isra'ila wanda ke neman nuna Turkiyya a matsayin tushen barazana," in ji Erdoğan.
"Muna kimanta wannan magana da cewa tana da alaƙa da tsarin siyasar cikin gida na Isra'ila da yanayin zaɓe na yanzu. Ba ma ɗaukar irin wannan tattaunawa a matsayin hanyar da ta dace wadda ke ba da gudunmawa ga zaman lafiyar yankin."
Zaman lafiyar Syria
Erdogan ya kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai a Syria, yana mai cewa cigaban da ake samu a kasar zai yi tasiri mai yawa ga yankin.
Ya ce, "Kwanciyar hankali a Syria zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da cigaban yankinmu baki ɗaya, ciki har da Isra'ila."
Erdogan ya ce shigar da dukkan masu dauke da makamai ƙarƙashin tsarin ƙasa mai ƙarfi yana da muhimmanci don ƙarfafa ikon mallakar Syria, mutuncin yankuna da haɗin kan zamantakewa.
"Muna goyon bayan wannan tsari na cigaba bisa ga yin adalci tsakanin ‘yan ƙasa, tare da haɓaka tsari wanda dukkan mutanen Syria - gami da Kurdawa - za su samu aminci, 'yanci, da wadata," in ji shi.
"Yayin da haɗin kan Syria ke ƙara ƙarfi, haka ma tsaron yankinmu zai yi ƙarfi."
Al’amuran da ke faruwa a Iran
Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya na ci gaba da sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a makwabciyarta Iran, ciki har da abin da ya kira yunkurin kungiyar 'yan ta'adda ta PKK/PJAK na yin amfani da halin da ake ciki a kasar.
"Muna kuma sa ido sosai kan yunkurin PKK/PJAK na yin amfani da yanayin da ya samo asali daga abubuwan da ke faruwa a Iran. Dole ne al'umar Iran da kansu su warware matsalolin cikin gida na kasarsu, ba tare da tsoma bakin kasashen waje ba," in ji shi.
Erdogan ya jaddada cewa tsarin da Turkiyya ke bi wajen tabbatar da tsaron yankin ba ya dogara kan bambancin kabila.
"Abin da Turkiyya ke la'akari da shi ba shi ne kabila ba; abin da take dubawa shi ne ta'addanci, tashin hankali, da barazanar da ke shafar tsaron kasarmu," in ji shi.
"Mun yi imanin cewa bai kamata a taba barin wata al'uma a yankinmu ta zama makamin yakin wasu kasashen waje a yankinmu ba."


















