| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Kotun Nijeriya ta ba da umarnin ƙwace kadarorin Aisha Achimugu na kusan Naira biliyan 9
Kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da kayan ado da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.645, motoci 11 na alfarma da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.293, da kuma dala 50,000 da Naira miliyan 30 lakadan.
Kotun Nijeriya ta ba da umarnin ƙwace kadarorin Aisha Achimugu na kusan Naira biliyan 9
Binciken ya fara ne bayan EFCC ta samu bayanan sirri kan shige da fitar kuɗi masu yawa cikin fiye da asusun banki 136 da ake dangantawa da Achimugu

Babbar Kotun Babban Birnin Tarayyar Nijeriya da ke zamanta a Apo, Abuja, ta bayar da umarnin ƙwace kayayyakin ado waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da ‘yan-kunne, agoguna, motocin alfarma da kuɗaɗe da ake dangantawa da 'yar kasuwa Aisha Achimugu, tare da mayar da su mallakin Gwamnatin Tarayya.

Mai shari'a Jude Onwuegbuzie ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 16 ga Yulin 2026, inda ya amince da buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC na ƙwace kadarorin har abada, bayan hukumar ta bayyana cewa an samo su ne daga haramtattun ayyuka.

Kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da kayan ado da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.645, motoci 11 na alfarma da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.293, da kuma dala 50,000 da Naira miliyan 30 lakadan.

A cewar EFCC, binciken ya fara ne bayan da ta samu bayanan sirri kan shige da fitar kuɗi masu yawa cikin fiye da asusun banki 136 da ake dangantawa da Achimugu, inda aka yi mu'amalar biliyoyin naira da miliyoyin daloli.

Hukumar ta ce bincikenta ya nuna cewa kuɗaɗen da suka riƙa shiga da fita ta kamfanonin da ake dangantawa da 'yar kasuwar ba a bayyana su a matsayin kuɗaɗen shiga a bayanan kuɗin da aka miƙa wa Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS) ba. Ta kuma ce binciken da aka gudanar a gidan Achimugu ya kai ga gano kadarorin da aka ƙwace.

EFCC ta ƙara da cewa duk da cewa Achimugu ta cike takardar bayyana kadarorinta yayin da ake yi mata tambayoyi, ba ta bayyana waɗannan kadarorin da aka gano ba. Hukumar ta ce bincikenta ya nuna cewa kuɗaɗen da suka shiga asusun da ake dangantawa da ita ba su fito daga halastattun harkokin kasuwancinta ba, kuma an samo kadarorin ne daga hanyoyin da ba su dace da doka ba.

Bayan kammala binciken, EFCC ta hannun tawagar lauyoyinta ƙarƙashin jagorancin Babban Lauya, Ekele Iheanacho (SAN), ta nemi kotu ta bayar da umarnin ƙwace kadarorin na wucin-gadi bisa Sashe na 17 na Dokar Zamba ta Advance Fee Fraud da Sauran Laifuka masu Alaƙa. A ranar 23 ga Afrilun 2026, kotun ta amince da buƙatar tare da umartar EFCC ta wallafa umarnin a jaridun ƙasa domin duk mai da'awa kan kadarorin ya bayyana cikin kwanaki 14 dalilin da ya sa ba za a ƙwace su har abada ba.

Achimugu ta hannun lauyoyinta ta ƙalubalanci umarnin na wucin-gadi tare da gabatar da takardun rantsuwa na nuna dalilin da ya sa bai kamata a ƙwace kadarorin ba. EFCC ta mayar da martani da nata takardun rantsuwa, bayan haka ɓangarorin biyu suka gabatar da hujjojinsu a gaban kotun.

A hukuncinta, kotun ta ce Achimugu ta gaza karyata hujjojin da EFCC ta gabatar, kuma ba ta iya tabbatar da cewa an mallaki kadarorin ta halastacciyar hanya ba. Saboda haka, Mai shari'a Onwuegbuzie ya bayar da umarnin ƙwace kayan ado, motocin alfarma da kuɗaɗen tare da mayar da su mallakin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.