| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Matatar Dangote ta koma amfani da farashin dala don sayar da manta maimakon naira
Tun a Oktoban 2024 ne matatar ta shiga shirin sayan ɗanyen mai daga Nijeriya kan farashin naira, sannan ta sayar da tataccen mai a naira, wanda aka ci gaba da sabuntawa lokaci bayan lokacin.
Matatar Dangote ta koma amfani da farashin dala don sayar da manta maimakon naira
A baya Matatar Dangote ta shiga shirin amfani da farashin naira tare da gwamnatin Nijeriya.

Matatar Dangote a Nijeriya ta fara saka farashin dalar Amurka kan man da take sayarwa ga masu buƙata a defo ɗinta, inda farashin mai samfurin PMS yake a dala $0.779 duk lita.

Sauyin salon tsayar da farashin tataccen mai daga naira zuwa dala ya fara aiki ne ranar Litinin 13 ga Yuli, kuma ya shafi man dizal wanda ya koma $1.087 duk lita.

Sai kuma man jiragen sama wanda ya tsaya kan $0.942 duk lita. Nau’in man LPG ne kawai sauyin bai shafa ba.

Bayanin wannan sabon farashin ya zo ne a wata sanarwa da aka aike wa dillalan mai, wadda kuma ta jaddada cewa sabon tsarin ya soke duk wata oda da aka yi kan farashin naira.

Masu AlakaTRT Afrika - Matatar man Dangote ta sayar wa Saudiyya man jiragen sama

Wannan na nuna cewa an kawo ƙarshen shirin Matatar Dangote da gwamnatin Nijeriya na sayar da ɗanyen man ƙasar kan farashin naira ga matatar, domin matatar ta sayar da tataccen mai kan naira a ƙasar.

Tun a Oktoban 2024 ne matatar ta shiga wannan shiri, wanda aka ci gaba da sabuntawa lokaci bayan lokacin saboda yana amfanar ‘yan Nijeriya da kuma tattalin arziƙin ƙasar.

A zahiri dai, sabon tsarin na yanzu zai sa matatar Dangote ta daidaita farashin ɗanyen mai da take saya wanda yawancin yana zuwa ne kan farashin dala, ya yi daidai da farashin tataccen mayukan da take sayarwa.

Masu lura da harkokin makamashi a Nijeriya suna cewa wannan mataki na matatar wani babban sauyi ne ga ayyukan cinikayyar mai, wanda zai iya tasiri ga kasuwancin mai a ƙasar saboda matatar ita ce ta fi samar da mai a ƙasar.

Yanzu dai za a jira ganin wane tasiri wannan zai yi kan farashin mai a gidajen mai da ke cikin Nijeriya, kasancewar da ma an samu hauhawar farashin mai a ‘yan watannin nan.