Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce ɗaukar fansa kan kisan da aka yi wa mahaifinsa, Ali Khamenei, "buƙatar ƙasa" ce kuma "dole ne " a aiwatar da ita.
Ya yi waɗannan kalamai ne a cikin wani saƙo da aka gabatar yayin jana’izar marigayi Jagoran Addinin Iran, in ji kafar watsa labaran ƙasar IRIB.
"Mun sha alwashin ɗaukar fansa kan zubar da jininka mara laifi da kuma na dukkan shahidai na yaƙe-yaƙe biyun nan daga masu kisan kai, masu aikata laifuka marasa matuncin," kamar yadda Mojtaba Khamenei ya bayyana a cikin saƙon.
"Wannan lamarin ba ya dogara kan rayuwata ta kaina ko kuma kan sauran jami’ai. Ko muna nan ko ba ma nan, zai faru."
An binne Ali Khamenei ranar Alhamis a Hubbaren Imam Reza a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, lamarin da ya kawo ƙarshen mako ɗaya na gagarumar jana’izarsa.

An kashe shi ne a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar farko ta yaƙinsu wanda aka fara ranar 28 ga watan Fabrairu.
Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin Amurka da sauran wurare da ke ƙasashen Larabawa.
Wani rahoton da jaridar The Wall Street Journal ta wallafa ranar Alhamis ta ce kwanan ne Isra’ila ta miƙa wa Amurka bayanan sirri da ke iƙirarin cewa Iran ta kitsa sabon shiri na kashe Shugaban Amurka Donald Trump.
A wani saƙon da ya wallafa ranar Jumma’a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, Trump ya yi barazanar ƙaddamar da hare-haren "dubban makamai masu linzami" kan Iran idan ta yi ƙoƙarin kashe shi.
A watan Yuni, Tehran da Washington sun rattaɓa hannu kan wata takardar fahimtar juna da Pakistan ta jagoranci samar da ita da zummar kawo ƙarshen yaƙin da aka fara a ƙarshen watan Fabrairu da kuma buɗe hanya ga yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa.
Takardar ta fahimtar juna ta yi kira ga kawo ƙarshen faɗa nan-take a dukkan fagen yaƙi da janye ƙawanyar sojin ruwa kan Iran da kuma sake buɗe mashigar ruwan Hormuz.
Duk da yarjejeniyar, ɓangarorin biyu sun yi musayar hare-hare a cikin wannan makon game da wucewar jiragen ruwa na ‘yankasuwa ta mashigar ruwan Hormuz.
Amurka ta kai hari kan wurare a Iran, wadda ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan kayayyakin Amurka a faɗin yankin.

















