Matar shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga Saudiyya da ta tallafa wajen faɗaɗa damar samun ilimin zamani ga almajirai da waɗanda ba sa zuwa makaranta, tana mai cewa matakin zai iya taimakawa wajen magance rashin tsaro da kuma inganta makomar ƙasar.
Da take magana a lokacin da ta karɓi baƙuncin Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Yousef Mohammed Al-Balawi, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Alhamis, Oluremi ta ce akwai buƙatar Nijeriya ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Masarautar Saudiyya don gyara tsarin ilimin almajirai ta hanyar haɗa karatun Musulunci da na zamani.
Ta ce wannan tsari zai samar wa yara marasa galihu, musamman waɗanda ke yankin arewacin Nijeriya, ingantattun damarmaki na ilimi tare da bin tsarin koyarwar addinin Musulunci.
"Ina aiki da mata da yara marasa galihu, amma ina matuƙar tausaya wa yara almajirai a arewacin Najeriya. Sun cancanci samun kulawa mafi kyau," in ji matar shugaban ƙasar.
Ta yi gargaɗin cewa rashin magance buƙatun almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta zai iya ta'azzara ƙalubalen tsaro a Nijeriya.
"Idan muka iya samar musu ilimin zamani da na addini, za a samu tsaro a makomar Nijeriya," in ji ta
Kazalika Oluremi ta yi jinjina bisa daɗaɗɗiyar dangantakar diflomasiyya tsakanin Nijeriya da Saudiyya, sannan ta bayyana fatan samun haɗin gwiwa mai zurfi a fannin ilimi da sauran fannoni.
A nasa ɓangaren, jakadan Saudiyya Al-Balawi ya ce ya samu ƙwarin gwiwa daga kyakkyawar tarbar da ya samu tun lokacin da ya isa Nijeriya watanni biyar da suka gabata.
Ya ce tattaunawa da yi da jami'an gwamnatin Nijeriya sun ƙara ƙarfafa dangantaka da ke tsakanin ƙasashen biyu, haka kuma ya nuna ƙwarin gwiwar ci gaba da faɗaɗa haɗin gwiwa.
"Dangatakar ƙasashenmu tana da tarihi mai tsawo, musamman ta fannin addini da al'adu, da kuma yiwuwar zurfafa haɗin gwiwarmu," in ji jakadan yana mai ƙari da cewa a “ƙasashen biyu suna da burin ƙarfafa tattalin arzikinsu.”
Al-Balawi ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan ofishin jakadancin Saudiyya a Nijeriya, Mohammed Bukar.


















