| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda' fiye da 300 a Zamfara
Hukumomin sun ce an cim ma ''nasarar'' ce bayan dakarun sun ƙaddamar da samame a sansanonin masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara.
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda' fiye da 300 a Zamfara
Nijeriya ta shafe kusan shekaru 20 tana fama da matsaloli na tsaro

Dakarun Nijeriya sun kashe masu garkuwa da mutane da satar shanu fiye da 300 a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar a wannan makon, kamar yadda wani jami’in jihar ya bayyana ranar Jumma’a.

Dakarun sun kai samame maɓoyar ‘yanbindigar da ke ƙaramar hukumar Gummi a wani aiki na kwanaki biyu lamarin da ya "kai ga kashe ‘yan ta’adda fiye da 300," kamar yadda kwamishinan watsa labarai na jihar Zamfara Mahmud Muhammad Dantawasa ya bayyana a wata sanarwa.

Ƙungiyoyin ta’addanci da "ɓarayin daji" da suka ƙware a garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suna yawan kai hare-hare a arewaci da tsakiyar Nijeriya tare da kisa da kuma ƙaƙaba haraji kan manoma da ke son zuwa gonakinsu.

Abubakar Muhammad, wani mazaunin Gummi, ya ce sojoji da ‘yan sa-kai sun yi arangama da kimanin ɓarayin daji 1,000 da ke ƙauracewa daga sansaninsu tare da ɗaruruwan dabbobi da suka sato da yammacin ranar Laraba zuwa ranar Alhamis.

Dawowar dakaru

"Sojojin da kuma ‘yan sa-kai sun kashe fiye da ɓarayin daji 300 a fafatawar da aka shafe dare zuwa safiya ana yi," kamar yadda Muhammad ya shaida wa AFP.

Abubakar Kudi-Kasa, wani mazaunin yakin, ya ce samamen ya faru ne da misalin ƙarfe 2130 agogon GMT ranar Laraba, kuma ƙarar harbi da fashewar ababe sun hana garin barci a cikin dare.

"Kawo yanzu sojoji da ‘yan sa-kai sun yi wa ɓarayin daji ƙawanya," kamar yadda Kudi-Kasa ya shaida wa AFP.

Dakaru sun yi ƙoƙarin mamaye sansanin ɓarayin makonnin biyu da suka wuce, amma dole suka ja da baya domin "tsabar yawan ɓarayi masu makamai da yawa", in ji Kudi-Kasa.

"Sojojin sun shirya da kyau kuma sun dawo domin kawar da su sosai."

Wani mazaunin wurin kuma Shehu Dandare ya ba da irin wannan adadin waɗanda suka mutun bayan dakaru sun "daka" ɓarayin.

‘Muhimmiyar nasara’

A watan Yulin shekarar da ta gabata, sojojin Nijeriya sun kashe aƙalla ɓarayin daji 150 a wani ƙwaton-ɓauna a wani babban ayarin kimanin ɓarayin daji 350 a jihar Kebbi da ke kusa yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Neja mai maƙwabtaka, kamar yadda jami’ai suka bayyana.

Bayan wata ɗaya, rundunar soji ta kashe fiye da ɓarayin daji 100 a ƙaramar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara, inda jiragen yaƙi tare da dakarun ƙasa suka far ma wani taron ɓarayin daji fiye da 400 a wani sansani na daji, in ji wani rahoton tsaron da aka haɗa wa Majalisar Ɗinkin Duniya.

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana samamen wannan makon a matsayin wata "muhimmiyar nasara" a yaƙin da ake yi da laifuka na hare-hare.

Nijeriya, ƙasar da ta fi yawan mutane a Afirka, tana fama da matsaloli na tsaro, ciki har da garkuwa da mutane da ‘yanbindiga ke yi.

Arewa maso gabashin Nijeriya na fama da ta’addanci tun shekarar 2009, daga farko daga hannun Boko Haram, daga baya kuma ƙugiyar Daesh da ta taso daga cikinta.