Faransa za ta fafata da Maroko a wani babban wasa wanda shi ne na farko a zagayen kwatafainal na Gasar Kofin Duniya na FIFA 2026.
Bayan kwashe wata guda ana wasanni masu ɗaukar hankali, inda aka zura ƙwallaye 280 cikin wasanni 96, a yanzu tawagogi 48 sun dawo saura takwas kacal, waɗanda ke ƙoƙarin lashe kofin a wasan ƙarshe ranar 19 ga Yuli a East Rutherford.
Faransa, wadda ta fi nuna bajinta a gasar zuwa yanzu, za ta fara zagayen kwata fainal tare da jarumar Afirka, Maroko a filin wasa na Gillette Stadium, a Boston, a wani wasa na maimaicin wanda suka buga a Kofin Duniya na 2022.
Rashin nasara ga tawagar Les Bleus zai kawo ƙarshen tafiyar da jagoran tawagar, Didier Deschamps, wanda zai yi murabus bayan shekaru 14 na nasarori a ƙarshen wannan gasa.
Deschamps, ɗaya daga cikin mutane uku kacal da suka taɓa lashe Kofin Duniya a matsayin ɗanwasa da kuma a matsayin mai horarwa, ya bayyana ranar Laraba cewa bai mayar da hankali kan kafa tarihin kansa ba.
Kocin na Faransa ya yi watsi da damuwar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, cewa zaɓin alƙalin wasa ɗan Argentina, Facundo Tello, zai iya jefa tawagarsa cikin matsala.
Faransa da Argentina suna kan hanyar yin karo a wasan ƙarshe a maimaicin fainal ɗin 2022, wanda Argentina ta yi nasara.
Da yake magana kan tawagar Maroko ƙarƙashin jagorancin Mohamed Ouahbi, Deschamps ya ce, “Mun fafata da su shekaru huɗu da suka gabata a samifainal, kuma Maroko ta buga wasan ƙarshe na gasar ƙasashen Afirka”.















