| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Rundunar Sojin Nijeriya ta kama jami'in da ake zargi da sayar wa 'yanta'adda kayan soji
A ranar 23 ga watan Yuli ne rundunar sojin Nijeriya ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zarginsa da sayar da kayayyakin aikin soji ga ‘yanta’adda da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
Rundunar Sojin Nijeriya ta kama jami'in da ake zargi da sayar wa 'yanta'adda kayan soji
Rundunar Sojin Nijeriya ta kama wani soja mai suna Mohammad Yusuf wanda ake nema ruwa-a- jallo bisa zargin sayar da kayan aikin soja ga 'yanta'adda

Sashen rundunar sojin Nijeriya na Operation HADIN KAI a yankin arewa maso gabashin ƙasar ya kama wani soja da ake nema ruwa-a-jallo bisa zarginsa da sayar da kayan aikin soji ga 'yanta'adda.

An kama wanda ake zargin mai suna Private Mohammed Yusuf da ke aiki a sashen samar da kayyakin kayan aikin sojin Nijeriya da ke Legas, a ranar Asabar a birnin Maiduguri na jihar Borno, yayin da yake yunkurin tserewa zuwa makwabciyar ƙasar Kamaru, kamar yadda wata sanarwa da rundunar Operation HADIN KAI ta fitar a ranar Lahadin nan da ta wuce.

A ranar 23 ga watan Yuli ne rundunar sojin Nijeriya ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zarginsa da samar da kayayyakin aikin soji ga ‘yanta’adda da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Masu AlakaTRT Afrika - Rundunar Sojin Nijeriya na neman jami'inta ruwa-a-jallo kan zargin sayar wa 'yanta'adda kayan soji

A cewar rundunar, tawagar dakarun 7 Provost na sojin ne suka kama jami’in a Jidari Bus Stop bayan sahihan bayanan sirri da ta samu, yanayin da rundunar ta bayyana a matsayin wani gagarumin ci gaba na yaki da ayyukan ta'addanci da ake ci gaba da yi.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya tsere daga wurin aikinsa a ranar 7 ga watan Yuli kafin ya koma Maiduguri, inda aka ce ya buya a yankin Gomari Costain da ke Ƙaramar Hukumar Jere tare da taimakon wani abokinsa.

Kazalika rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran ire-iren ayyukan da wanda ake zargin ya aikata tare da zakulo duk wanda ke da hannu a ciki.

Haka kuma rundunar ta ce kamen ya nuna irin tasirin ayyukan da hukumar leken asiri ke yi ta gudanar ya kuma kara jaddada kudurin rundunar sojin Nijeriya na ci gaba da daukar matakan da suka dace.

"Rundar Sojin Nijeriya za ta ci gaba da dagewa wajen tabbatar da kwarewa, da rikon amana da kuma nuna kishin kasa da gaskiya wajen gudanar da ayyukan yaƙi da ta'addanci," in ji sanarwar.