Hukumar zaɓen Nijeriya (INEC) ta ce za ta rufe damar sabuwar rijista ko gyara rijista ranar Lahadi 26 ga watan Yuli duk da kiraye-kirayen da wasu jam’iyyun adawa da masu fafatuka ke yi na tsawaita lokacin bisa damuwar cewa miliyoyin ‘yan ƙasar za su iya rasa damar zaɓe a zaɓukan 2027.
Rahotanni daga Nijeriya na cewa jam’iyyun adawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun nemi a tsawaita rijistar domin bai wa ƙarin ‘yan Nijeriya da suka kai yin zaɓe damar rijista, yayin da hukumar zaɓe INEC ke kira ga sauran waɗanda ba su yi rijista ba su yi amfani da sa’o’in da suka saura kafin cikan wa’adin ranar Lahadi domin yin rijistar.
A wani saƙon da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi, hukumar ta ce za a rufe rijistar ranar Lahadi 26 ga watan Yuli inda ta ce mutane za su iya ƙarƙare rijistarsu ta intanet cikin sa’o’in da suka saura.
“Lokaci na ƙurewa, amma akwai dama ta iya sa a ji muryarka,” in ji saƙon da INEC ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi.
Dokar zaɓen Nijerira ta bai wa INEC ƙa’idar dakatar da sabuwar rijista da gyara rijista kwanaki 90 kafin zaɓe domin tsaftace bayananta da kuma buga sabbin katunan zaɓe na din-din-din da sauran shirye-shiryen zaɓe.
Dokar ta kuma buƙaci hukumar ta fitar da bayanan waɗanda suka yi rijista domin ba da dama ga iƙirari da kuma inkari a cikin lokacin don ‘yan Nijeriya su iya ƙalubalantar kurakurai don tabbatar da sahihancin rijistar gabanin zaɓe.
INEC ta kore yiyuwar tsawaita lokacin
Jaridar Punch ta Nijeriya ta ambato ƙwamishanan INEC, Mohammed Haruna, yana cewa hukumar ba za ta tsawaita wa’adin rufe rijistar ba, yana mai jaddada cewa dole a rufe rijistar domin bai wa hukumar damar fara tsaftace bayanan da ta riga ta tattara.
“Daga Misalin ƙarfe 12 na dare ranar Lahadi, rijistar masu zaɓe zai ƙare. Ba za a tsawaita ba ta ba. Akwai ababe da yawa da muke buƙatar yi a bayan fage. Dole mu shata layi; idan ba haka ba za mu iya samar da wani tsaftataccen kwafi na abin da aka riga aka tura ba,” in ji shi.
Haruna ya bayyana cewa ɓangaren fasahar sarrafa bayanai da kuma rijistar masu zaɓe za su fara sarrafa bayanan nan take bayan lokacin rufe rijistar.
Jam’iyyun ADC da PDP da masu fafatuka sun buƙaci tsawaita lokacin rijistar
Sakataren watsa labaran jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya shaida wa jaridar Punch cewa bai kamata a alƙanta rijistar zaɓe da wani wa’adi ba.
Ya ce ya kamata a ce ‘yan Nijeriya suna da wata dama wadda ke a buɗe kusan ko a wane lokaci ta iya yin rijista a ko wane lokacin da suka so yin zaɓe.
“Mun gayyaci mutane a faɗin ƙasar zuwa rijistar INEC, amma ka san abu mai wuya ne mutane su yi watsi da ayyukansu na yau da kullum su je su bi layi a ofisoshin INEC domin rijista. Abin da muka yi shi ne mu gayyaci mutanenmu da ke matakin karkara,” in ji shi.
Kazalika, sakataren watsa labarai na kwamitin riƙo da Jam’iyyar PDP ɓangaren Tanimu Turai, ya shaida wa Punch cewa ya kamata hukumar ta mayar da hankali kan haɗa kowa a rijistar ta hanyar tsawaita lokacin rijistar.
Kazalika jairdar ta ambato masu fafatuka suna kira ga hukumar cewa ta bai wa sauran ‘yan ƙasar da ba su yi rijista ba damar rijista ko kuma gyara rijistarsu ta hanayr tsawauta wa’adin rufe rijistar.


















