| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
4 minti karatu
An kai wa ma'aikatan jiragen ruwan India hari kusa da mashigar Hormuz
New Delhi ta ba da rahoton cewa wani hari kan wani jirgin dakon kaya na 'yan kasuwa a Bahar Aswad ya kashe wani ɗan India, yayin da aka kai hari kan wani jirgin ɗauke da iskar gas da ma'aikatan jiragen ruwan India 28 a cikin ruwan Iran.
An kai wa ma'aikatan jiragen ruwan India hari kusa da mashigar Hormuz
Mashigar Hormuz wata hanyar ruwa ce tsukakkiya 21 inda kashi 20 cikin 100 na man duniya da kimanin kashi 20 cikin 100 na iskar gas ke wucewa

India ta ce an kashe ɗaya daga cikin ‘yan ƙasarta a wani harin da aka kai kan wani jirgin ruwa na dakon kaya da ke wucewa ta Bahar Aswad a makon da ya gabata.

New Delhi ta ƙara da cewa an kai hari kan wani jirgin ruwa ɗauke da iskar gas mai tutar Mozambique wanda ke da ma’aikata ‘yan India 28 a cikin ruwan Iran ranar Jumma’a.

Ma’aikatar harkokin wajen India ta yi Allah wadai da harin na Bahar Aswad ranar Jumma’a, tana mai cewa jirgin mai suna MV Omorfi — wanda ke ɗauke da ‘yan India uku — an kai masa hari ne ranar 18 ga watan Yuli "yayin da yake wucewa ta Bahar Aswad, inda rahotanni suka ce yana cikin ruwan Rasha ".

"India ta yi Allah wadai da irin waɗannan hare-haren kan jiragen ‘yan kasuwa da kuma barazana ga rayukan fararen hula ma’aikata," a cewar ma’aikatar a wata sanarwa.

"Wani abin damuwa ne matuƙa cewa ‘yancin wucewa ta ruwa da kuma kasuwanci na ƙasa da ƙasa na fuskantar ƙarin barazana."

A ranar Alhamis New Delhi ta fitar da gargaɗi ga jiragen ruwa masu tafiya Bahar Aswad da ke ɗauke da tutarta ko kuma ke da ma’aikatan jiragen ruwa ‘yan India, bayan an kashe huɗu daga cikin ‘yan ƙasarta a wani harin Rasha kan wani jirgin dakon kaya da ke barin Ukraine.

India ta kira babban jakadan Rasha a New Delhi domin nuna rashin jin daɗinta game da harin.

An kai hari kan Tanka ɗauke da ‘yan India 28

Kazalika ranar Jumma’a, an kai hari kan wani jirgin ruwa mai tutar Mozambique ɗauke da iskar gas da kuma ma’aikata ‘yan India 28 a cikin ruwan Iran, in ji ofishin jakadancin India a Tehran.

Dukkan ma’aikatan ‘yan India sun tsira kuma ofishin jakadancin na tuntuɓar hukumomi, kamar yadda ofishin ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.

Jirgin mai suna Disha, wani makami mai linzami da ba sani ba ne ya kai masa hari kusa da mashigar Hormuz yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa yankin Gulf, in ji ƙungiyar ƙwadago ta ma’aikatan jiragen ruwa ta India a wani saƙon da ta wallafa a shafin X.

A wani ɓangare daban kuma, kafar watsa labaran ƙasar Iran ta ba da rahoton cewa wani makami mai linzamin Amurka ya far ma wani jirgin ruwa ɗauke da iskar gas da ya nufi Mashigar Hormuz inda ya kashe ma’aikata biyu bayan ya zaci jirgin na ɗauke da gas ɗin Iran ne.

Da take ambato wata majiya da ke da sani game lamarin, kafar IRIB ta ce sojojin Amurka sun harba makamai masu linzami biyu kan jirgin ranar Jumma’a yayin da take matsawa kusa da yankin daga tekun Oman.

Rahoton ya ce an kai wa jirgin hari ne saboda dakarun Amurka sun yi imanin cewa yana ɗauke da iskar gas ɗin Iran ne.

Kawo yanzu dai sojojin Amurka ba su yi tsokaci game da iƙirarin ba. Kuma babu tabbacin ko Iran tana magana a kan jirgin ruwan da India ta yi magan a kansa ne ko kuma wani jirgin na daban.

‘Yan India shashida ne aka kashe ko kuma suka ɓata a Gabas Ta Tsakiya tun lokacin da aka fara yaƙin Amurka da Iran, in ji majiyoyin gwamnatin India.

Mashigar Hormuz, tsakanin Iran da Oman, ita ce muhimmiyar hanyar da kashi ɗaya cikin biyar na man duniya ke wucewa kafin ɓarkewar rikici a Iran.

Tashe-tashen hankula suna ƙaruwa tun lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni tsakanin Washington da Tehran ta wargaje a farkon watan Yuli, lamarin da ya farfado da musayar hare-hare masu ƙarfi da kuma ƙara katse jigilar kayayyaki ta hanyar ruwan.