| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An gudanar da zanga-zanga a Tripoli saboda tsadar rayuwa da tabarbarewar ayyukan gwamnati
Masu zanga-zangar sun yi tir da matsalar wutar lantarki, yawan katsewar ruwa, raunin tsarin kiwon lafiya da kuma hauhawar farashin kayayyaki, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Libya.
An gudanar da zanga-zanga a Tripoli saboda tsadar rayuwa da tabarbarewar ayyukan gwamnati
Zanga-zangar ta zo ne yayin da Libya ke fama da matsanancin zafi na kwanaki da dama / Reuters Archive

An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na babban birnin Libya, Tripoli, daga daren Lahadi zuwa ranar Litinin saboda taɓarɓarewar yanayin rayuwa da kuma gazawar ayyukan gwamnati, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na hukumomin ƙasar suka ruwaito.

Masu zanga-zangar sun yi tir da matsalar wutar lantarki, yawan katsewar ruwa, raunin tsarin kiwon lafiya da kuma hauhawar farashin kayayyaki, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Libya (LANA).

Masu zanga-zangar sun ƙone tayoyin motoci a yankunan Tajoura, Souq al-Jumaa, Al-Sarraj, Janzour, Zawiyat al-Dahmani da Al-Dhahra, tare da rufe mahadar tituna, in ji kamfanin dillancin.

Sun kuma kafa shingaye a gaban wasu cibiyoyin gwamnati, ciki har da Ma'aikatar Harkokin Waje da kuma Babban Gidan Talabijin na Libya da ke yankin Zawiyat al-Dahmani.

An kuma kafa shingaye a gaban ginin Hukumar Binciken Kuɗi da hedikwatar Hukumar Kula da Sadarwa a yankin Al-Nofliyeen.

Zanga-zangar ta zo ne yayin da Libya ke fama da matsanancin zafi na kwanaki da dama, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki na fiye da sa'o'i 14 a wasu unguwanni.

Masu zanga-zangar sun riƙa rera taken da suka haɗa da: "Al'umma na son adalcin da zai hukunta waɗanda suka wawure kuɗaɗensu," "Kuɗin al'umma amana ce a hannunku," da kuma "Ina wutar lantarki? Ina biliyoyin kuɗin suka tafi?"

Gwamnatin Haɗin Kan Ƙasa (Government of National Unity) ƙarƙashin jagorancin Abdulhamid Dbeibeh ta ce tun daga shekarar 2021 take ƙoƙarin magance matsalar wutar lantarki, wadda ta samu gagarumin sauƙi tsakanin 2023 da 2025.

Har yanzu Libya na da gwamnatoci biyu masu hamayya: Gwamnatin Haɗin Kan Ƙasa, wadda duniya ta amince da ita ƙarƙashin jagorancin Dbeibeh mai hedikwata a Tripoli, wadda ke kula da yammacin Libya; da kuma gwamnatin da Majalisar Wakilai ta naɗa a farkon shekarar 2022, wadda Osama Hammad ke jagoranta kuma ke da hedikwata a Benghazi, wadda ke kula da gabashin ƙasar da mafi yawan kudancin Libya.

Shekaru da dama kenan Ofishin Tallafa wa Majalisar Ɗinkin Duniya a Libya (UNSMIL) ke ƙoƙarin sasanta rikicin siyasa domin a gudanar da zaɓe, wanda 'yan Libya da dama ke fatan zai kawo ƙarshen rarrabuwar kawunan siyasa da rikicin makamai da ƙasar ke fama da shi tun bayan hamɓarar da Muammar Gaddafi a shekarar 2011.