| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Rasha na son ƙarfafa alaƙa da Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) - Lavrov
"Muna da fahimta iri ɗaya kan buƙatar gina tsarin duniya na adalci mai rassa da yawa, da kuma haɗin gwiwarmu wajen yaƙi da dabarun sabon mulkin mallaka, waɗanda har yanzu suke tare da ƙawayenmu na Yammacin duniya," in ji Lavrov.
Rasha na son ƙarfafa alaƙa da Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) - Lavrov
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov da jami'an AES a birnin Yamai don taron ministoci, ranar 8 ga Yulin 2026. / Reuters / Reuters

Ministan Harkokin Ƙasashen Waje na Rasha, Sergey Lavrov, ya bayyana a ranar Laraba cewa Moscow na son ƙarfafa haɗin gwiwa da Ƙungiyar Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) wajen tallafa wa ƙoƙarin dunƙulewar ƙasashen da mayar da hankali kan batutuwan tsaro.

Da yake jawabi a wajen buɗe taron tuntuɓa na biyu na ministoci tsakanin Rasha da Kungiyar Kawancen Kasashen Sahel a Jamhuriyar Nijar, Lavrov ya ce ɓangarorin biyu suna da mahanga guda kan samar da "tsarin duniya na adalci mai rassa da yawa" da kuma adawa da "tsarin sabon mulkin mallaka."

"Muna da fahimta ɗaya kan buƙatar gina tsarin duniya na adalci mai rassa da yawa, da kuma haɗin gwiwarmu wajen yaƙi da dabarun sabon mulkin mallaka, waɗanda har yanzu suke tare da ƙawayenmu na Yammacin duniya," in ji Lavrov.

Ya bayyana cewa Rasha na fatan haɗin gwiwarta da ƙungiyar za ta karfafa ikon cin gashin kan ƙasashen, sannan ya faɗaɗa alaƙar cin moriyar juna ta bangarori daban-daban.

Lavrov ya kuma sanar da cewa za a gudanar da Babban Taron Rasha da Afirka karo na uku a birnin Moscow a watan Oktoba, inda ajandar taron za ta mayar da hankali kan haɗin gwiwar tattalin arziki, da kasuwanci, da zuba jari.

Ya ƙara da cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin ya buƙace shi da ya gayyaci shugabannin ƙasashen Burkina Faso, da Mali, da Nijar domin su halarci taron.

Haka zalika, Moscow na sa ran ministoci da wakilan 'yan kasuwa daga kasashen uku za su halarci taron Tattalin Arziki da Jinƙai da za a gudanar a lokacin.