Yadda matsalar tsaron Nijeriya ke ƙara barazana ga wadatar abinci
NIJERIYA
3 minti karatu
Yadda matsalar tsaron Nijeriya ke ƙara barazana ga wadatar abinciA cikin watan Yunin da ya gabata kaɗai, rahotanni sun bayyana cewa an kashe manoma fiye da 100 a hare-hare daban-daban da aka kai a jihohi da dama.
Hare-hare na zuwa ne a muhimmin lokaci na damina, abin da ke ƙara haifar da damuwa kan yiwuwar raguwar amfanin gona, da tashin farashin abinci. / Reuters

Rashin tsaro a arewacin Nijeriya na ƙara ƙamari inda a cikin ‘yan kwanakin nan ‘yan ta’adda a jihohi daban-daban na arewacin ƙasar suka rinƙa bin manoma har gonakinsu suna kashe su, lamarin da ke ƙara bayyana irin matsalar rashin tsaro da ke addabar yankunan karkara da kuma tasirin matsalar ga samar da abinci.

A cikin watan Yunin da ya gabata kaɗai, rahotanni sun bayyana cewa an kashe manoma fiye da 100 a hare-hare daban-daban da aka kai a jihohi da dama.

A Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, an kashe manoma 17, yayin da wasu 15 suka rasa rayukansu a Talata Mafara.

A Jihar Borno, an ruwaito kashe manoma 11 a ƙauyen Kuwawu, yayin da aƙalla mutum 20 suka mutu a Bokkos da ke Jihar Filato. A Jihar Neja kuma, mutum 42 suka mutu a wani hari da makiyaya suka kai a Ƙaramar Hukumar Rafi.

Hare-haren sun faru ne a yankuna daban-daban na ƙasar, kuma ana danganta su da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai daban-daban, ciki har da ɓarayin daji, 'yan ta'addan Daesh da sauran masu aikata laifuka da ke kai hare-hare a yankunan karkara.

A lokuta da dama, manoma ne ake kai wa hari yayin da suke aiki a gonakinsu ko girbin amfanin gona ko kuma a hanyarsu ta zuwa ko dawowa daga gonaki.

Masana harkokin tsaro sun ce hare-haren da ake ci gaba da kaiwa ba wai kawai suna salwantar da rayuka ba ne, amma suna kawo cikas ga harkokin noma, suna hana mutane komawa gona, tare da yin barazana ga samar da abinci a ƙasar da miliyoyin mutane ke dogaro da noma domin samun abin rayuwa.

Wadannan hare-hare na zuwa ne a muhimmin lokaci na damina, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa kan yiwuwar raguwar amfanin gona, tashin farashin kayan abinci da kuma tsananta halin ƙuncin rayuwa a al'ummomin da tuni suke cikin mawuyacin hali.

Duk da cewa jami’an tsaro sun ƙara kaimi wajen kai hare-hare kan ‘yanta’dda a sassa daban-daban na ƙasar, jama’ar karkara da shugabanninsu na ci gaba da kira da a ɗauki ƙarin matakai masu ƙarfi domin kare al'ummomin manoma da tabbatar da cewa mutane za su iya komawa gonakinsu cikin aminci.

Ga al'ummomi da dama na karkara, damar yin noma ba tare da fargaba ba na ƙara zama mai wahala, abin da ke nuna irin babbar barazanar da rashin tsaro ke yi ga tattalin arzikin Nijeriya, wadatar abinci da kuma zaman lafiyar al'umma baki ɗaya.

Rumbun Labarai
Amurka ta janye akasarin sojojinta da ta aika Nijeriya
Yunwa ta kai mummunan mataki da bai taɓa kai wa ba a shekaru 10 a Arewacin Nijeriya - WFP
Sojojin Nijeriya sun kashe ’yanta’adda 662, sun ceto 951 da aka sace cikin watanni uku
CBN ya soke lasisin ƙananan bankuna na Microfinance 46 saboda rashin cika ƙa’idoji
Nijeriya ta yi alƙawarin tallafa wa 'yan ƙasar 271 da suka dawo daga Afirka ta Kudu
Ɗan Nijeriya ya mutu bayan sakinsa daga kurkuku a Côte d'Ivoire
Gwamnatin Nijeriya ta karɓi 'yan ƙasar 269 da aka sake mayarwa gida daga Afirka ta Kudu
Jam'iyyar adawa ta NDC a Nijeriya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu game da rajistarta
Sojojin Nijeriya sun ceto ɗalibai da malaman GDSS Lassa 10 a Jihar Borno
Dakarun Nijeriya sun ce manyan kwamandojin DAESH sun miƙa wuya sakamakon ƙara matsin lambar soji
An kama mutane 10 da ake zargi da kashe shugaban ƙungiyar Fulani ta MACBAN na jihar Benue a Nijeriya
Sojoji sun kashe Lakurawa biyu da ƙwato makamai a Arewa Maso Yammacin Nijeriya
DSS ta saki mutumin da aka tsare saboda zargin alaƙa da Boko Haram bisa kuskure, ta biya shi diyya
'Yanbindiga a Nijeriya sun kashe manoma 17 a Jihar Zamfara
An gurfanar da ƙarin mutum 17 bayan tuhumar 33 bisa zargin kisan Malamar Islamiyya a Kaduna
Sojojin Nijeriya sun ceto fararen-hula 53 tare da ƙwato motoci takwas a Borno
Mutum aƙalla takwas sun mutu, an ceto 26 bayan bene mai hawa uku ya rushe a Legas
Kotu a Nijeriya ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta rataya, ciki har da wani ɗan ƙasar waje
'Yansanda a Nijeriya sun kama 'yan kasashen waje 38, sun ƙwato makamai a jihar Legas
CBN ya ƙaddamar da jakadun kare martabar naira a ƙasar