Gwamnatin Nijeriya a ranar Lahadi ta ce an kashe ’yan ƙasarta biyu a watan da ya gabata a Afirka ta Kudu, sakamakon zanga-zangar adawa da baƙi wadda ake yi a ƙasar musamman domin ma’aikata ‘yan ƙasashen Afirka a ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta ce an kashe ’yan Nijeriyar ne a ranar 28 ga Yuni, kwanaki biyu kafin wani wa’adi da masu zanga-zangar suka saka wanda ba na hukuma ba don barin ƙasar ga baki.
’Yansandan Afirka ta Kudu ba su mayar da martani ba ko kuma amsa buƙatar ji ta bakinsu da kamfanin dillancin labarai na AP ya yi.
A watan Afrilu da Mayu, masu zanga-zangar adawa da baƙi sun zargi baƙin da haddasa matsanancin rashin aikin yi, aikata laifuka da kuma wahala kan ayyukan jama’a. Wannan tashin hankali ya sa Nijeriya, Ghana da Malawi suka mayar da ’yan ƙasashensu gida kuma suka kira jakadun Afirka ta Kudu.
A shekarar 2008, fiye da mutane 60 suka rasa rayukansu a Afirka ta Kudu a abin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama suka kira da ƙin jinin baƙi ‘yan ƙasashen waje.














