| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya za ta binciki manyan kamfanonin fasaha kan amfani da labaran ƙasar ba bisa ƙa’ida ba
Wata sanarwa da hukumar FCCPC ta Nijeriya ta fitar ta ce matakin ya biyo bayan wani koke da Kungiyar Kamfanonin Watsa Labarai ta Nijeriya NPO, wacce ke wakiltar manyan kungiyoyin kafafen yada labarai na ƙasar ta shigar.
Nijeriya za ta binciki manyan kamfanonin fasaha kan amfani da labaran ƙasar ba bisa ƙa’ida ba
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya bayar da umarnin gudanar da binciken / Reuters

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Kula da Gogayya da Kare Haƙƙin Masu Amfani da kayayyaki ta Nijeriya (FCCPC) da ta gudanar da bincike kan manyan kamfanonin fasaha—musamman Meta, Alphabet (Google), X, da wasu manyan manhajojin kirkirarriyar Basira ta AI—bisa zargin yin amfani da dabarun hana gogayya da kuma amfani da labaran kafofin watsa labaran Nijeriya ba bisa ka'ida ba.

Wata sanarwa da hukumar FCCPC ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba ta bayyana cewa, matakin ya biyo bayan wata takardar koke da Kungiyar Kamfanonin Labarai ta Nijeriya (NPO) ta shigar, wacce ke wakiltar manyan kungiyoyin kafafen yaɗa labarai na ƙasar.

"Hukumar FCCPC za ta tantance ko waɗannan dabarun sun keta Dokar Kare Gogayya ta Kasuwanci da Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki ta FCCPA ta shekarar 2018, ko kuma wasu dokoki masu alaƙa da hakan," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa, binciken zai kasance mai zaman kansa, a bayyane, kuma zai ginu ne a kan hujjoji, inda za a bai wa kowane ɓangare damar kare kansa cikin adalci. Sannan ba a riga an yanke wa kowa hukuncin daidai ko akasin haka ba tukunna.

Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa hukumar ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da adalci, inda ta bayyana cewa binciken na da nufin samar da daidaito tsakanin ci-gaban fasaha da kuma kare tsarin kafafen yaɗa labarai da ma tsarin demokuraɗiyyar Nijeriya.

Wannan matakin ya yi daidai da irin matakan da aka ɗauka a Afirka ta Kudu, inda kamfanin Google ya amince zai riƙa biyan kafafen yada labaran ƙasar kimanin dalar Amurka miliyan 40 duk shekara tsawon shekaru da dama, biyo bayan makamancin wannan korafi.