Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana alƙalin wasan da ya bai wa ɗanwasan Amurka Folarin Balogun jan kati a wasansu da Bosnia-Herzegovina a makon da ya gabta a matsayin wani “wanda ke da alamar tambaya” yayin da ake ci gaba da tayar da jijiyar wuya game da dakatar da jan katin da aka bai wa ɗanwasan .
Da yake magana a fadar White House ranar Litinin gabannin wasan zagaye na 16 da ƙasar za ta yi da Belgium, inda a halin yanzu za a bai wa Balogun damar buga wasa bayan an ɗage jingine hukuncin hana shi buga wasa ɗaya, shugaban ya ce: “Na ga wasan, ni wani mutum ne da yake ƙaunar wasanni...wannan ba ƙeta ba ce .
“Wannan ba laifi ba ne ma. Wanna alƙalin wasan, wanda da ke da alamar tambaya a kansa ne idan ka lura da tarhinsa . Ya yanke wani hukuncin da babu wanda zai iya yarda da shi. Ɗanwasanmu mafi ƙarewa ne, ko kuma ɗaya daga cikin ‘yanwasanmu da suka fi ƙwarewa. Kuma ya ba shi jan kati. A da ban san abin da hakan ke nufi ba...Da gaske na nemi FIFA ta sake nazari a kai.
“Ban san abin da ake ce wa jan kati ba. Da na gane, na ce, ‘Ba ka isa ba!’”
Hukumar FIFA dai ta yarda a ɗauke wa Balogun hukuncin hana shi buga wasan ƙasarsa da Belgium.
Bayan haka ne ƙasar Belgium ta kai ƙara FIFA tana neman hukumar ta ƙwallon ƙafa ta duniya ta hana ɗanwasan buga wasan da za su kara a zagaye na ƙsashe 16 na Gasar Cin Kofin Duniya.
Sai dai hukumar FIFA ta yi watsi da wannan ƙarar ta hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Belgium.










