| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Pezeshkian ya soki shirun duniya bisa matakan Isra'ila yayin da aka fara taron jana'izar Khamenei
Shugaban Iran ya soki hukumomin duniya a lokacin taron ban-girma ga tsohon Jagoran Addinin Ali Khamenei a Tehran.
Pezeshkian ya soki shirun duniya bisa matakan Isra'ila yayin da aka fara taron jana'izar Khamenei
Tawagogi daga ƙasashen ƙetare na halartar taron bankwana wa marigayi Jagoran Addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei / Reuters

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya soki hukumomin ƙasa da ƙasa bisa abin da ya kira gazawarsu wajen daƙile matakan Isra’ila a yankin, yana mai cewa hukumomin duniya sun ƙi cewa komai yayin da Isra’ila take magana a bayyana game kisan gilla da kuma kashe mutane ɗaɗɗaya.

Da yake magana a wani taro a Ɗakin Taron Tehran inda ake tunawa da tsohon Jagoran Addini Ali Khamenei da aka kashe, Pezeshkian ya ce an tsammanci hukumomin ƙasa da ƙasa da kuma hukumomin kare haƙƙin bil Adama su hana irin waɗannan matakan , amma maimakon haka , ana samar da tallafi na siyasa da na kaikomo ne.

Ya ce Isra’ila ta kai hari kan ƙasashe a yankin kuma ita ce ta haddasa yawancin rikice-rikice da rashin zaman lafiya a faɗin Gabas Ta Tsakiya , yana mai ƙarawa da cewa ƙasashen Musulmai ba su suka fara irin wannan tsokanar ba.

Sabon lokacin shugabanci

Pezeshkian ya kuma yi ishara ga farkon wani "sabon shugabanci" ga ƙasar , yana mai cewa shugabanci na yanzu na ɗauke da nauyi mai yawa kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki domin cim ma manufofin juyin juya hali da ƙarfafa haɗin kan Musulunci da kuma faɗaɗa haɗin kai tsakanin ƙasashen Musulmai.

Kalaman na zuwa ne yayin da aka fara taron jana’izar Khamenei a Tehran, inda dubban masu jimami suka hallara a Masallacin Jumma’an Imam Khomeini .

An kashe Khamenei ne a harin Amurka da Isra’’ila ranar 28 ga watan Fabrairu, lamarin da ya haddasa makonni na yaƙi kafin a cim ma tsagaita wuta a ƙarƙashin shiga-tsakani na Pakistan a watan Afrilu, inda yarjejeniyar wucen gadi ta biyo baya a watan Yuni.

Jerin-gwanon jana’iza a cikin birane

Jadawalin hukuma dai ya nuna cewa , za a ci gaba da tarukan tunawa a Tehran a cikin ƙarshen mako inda shugabannin ƙasashe za su hallara tare da manyan jami’ai da shugabannin addinai.

An shirya yin tarukan bankwana a fili ranar Asabar da Lahadi, waɗanda babban jerin-gwanon jana’iza zai biyo bayansu a Tehran ranar Litinin.

Tarukan jana’izar za su koma Qom ranar 7 ga watan Juli.

Ranar 8 ga watan Juli, an shirya yin taruka a Iraƙi, ciki har da Baghdad da Najaf da Karbala, inda jami’an addini da na siyasa za su karɓi gawar kafin a kai ta muhimman wuraren Shia.

Taron jana’iza ta ƙarshe da kuma bunne gawar an tsara yin su ne ranar 9 ga watan Juli a wurin ibada na Imam Ali Reza a birnin arewa maso gabashi na Mashhad, ɗaya daga cikin wurare mafi tsarki na Shia a Musulunci.