Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, ta amince da ɗanwasan gaba na tawagar Amurka, Folarin Balogun, ya buga wasan da za su kara da Belgium ranar Litinin a wasan zagaye na ‘yan-16 a Gasar Kofin Duniya.
Wannan na zuwa ne bayan FIFA ta ɗage hukuncin dakatarwa saboda jan kati da ya kamata ya hana Balogun buga wasa ɗaya, sakamakon amfani da Sashe na 27 na Dokar Ladabtarwa.
Mene Sashen Doka na 27?
Sashen Doka na 27 ya ba wa hukumomin shari'a na FIFA damar dakatar da aiwatar da duka ko wani ɓangare na hukuncin ladabtarwa.
Gundarin hukuncin yana ci gaba da kasancewa mai aiki a kan takarda, amma ba dole a aiwatar da shi nan-take ba sai dai idan daga baya an soke dakatarwar.
Dokar Ladabtarwar ba ta fayyace yanayin da hukumomin shari'a na FIFA za su iya yanke shawarar dakatar da hukunci ba.
Ana barin ɗanwasan yana jiran wa’adi tsakanin shekara ɗaya zuwa huɗu. Idan ya aikata irin wannan laifi a cikin wannan lokacin, kai-tsaye za a dawo da hukuncin da aka jingine, kuma za a ƙara masa sabon hukuncin ladabrtarwar.
An jinkirta hukuncin hana Balogun wasa ɗaya kuma an kafa masa lokacin jiran wa’adi na shekara ɗaya.
Kwamitin ladabtarwa
Hukunce-hukuncen ladabtarwar da ba za a iya dakatar da su ba su ne, waɗanda suka shafi karkatar da sakamakon wasa.
Hukumomin shari'a na FIFA sun haɗa da Kwamitin Ladabtarwa da Kwamitin Daukaka Kara.
Kwamitin Ladabtarwa ya ƙunshi shugaban kwamitin, mataimakin shugaban da sauran mambobi. Shugaban da mataimakin dole ne su kasance lauyoyi masu cancanta, kuma kwamitin na buƙatar aƙalla mambobi uku don yanke hukunci.
Mohammad Al Kamali daga Hadaddiyar Daular Larabawa, shi ne ke shugabantar Kwamitin Ladabi a halin yanzu. Ana zaɓar mambobin kwamitin ta hanyar Zaben Majalisar FIFA kan wa'adin shekaru huɗu, kuma za su iya yin wa'adi har uku.
A baya ana kiran Sashe na 27, da Sashe na 26, kafin a yi gyare-gyare ga Dokar Ladabtarwa a shekarar 2023.









