Matatar Man Fetur ta Dangote ta fara dakon fetur kyauta zuwa jihohi shida a faɗin Najeriya, ciki har da babban birnin tarayyar ƙasar, Abuja.
Kamfanin ya sanar da wannan sabon shiri ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta na X a ranar Laraba.
A cewar kamfanin, wannan hidima ta sufurin mai kyauta ta shafi jihohin Legas da Ogun da Rivers da Kaduna da Delta da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Kamfanin ya bayyana cewa wannan damar ta shafi abokan hulɗa ne kawai wadanda suka sayi akalla lita 50,000 ta man fetur.
Matakin na zuwa ne kakwanaki kaɗan bayan Matatar ta Dangote ta gana da masu ruwa da tsaki a fannin kasuwancin mai na ƙasa don tattaunawa kan samar da farashin fetur mai sauƙi da ya dace da kasuwa.
Taron ya kammala ne inda masu ruwa da tsakin suka nuna goyon bayansu ga yunkurin kara rage farashin man fetur.
Kafin wannan lokaci, kamfanin ya riga ya sanar da ragi na hudu a jere na farashinsa na sayar da fetur, inda ya dawo da shi N1,075 a kowace lita.







