Hukumar NDLEA mai yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a Nijeriya ta kama wata mata ‘yar ƙasar Afirka Ta Kudu mai shekara 38, Mis Will Jessica Ann, da ƙulli-ƙullin hodar iblis masu nauyin kilogiram 5.75 a cikin jakkunanta inda hukumar ta ce tana amfani da yaronta ɗan shekara 3 wajen kauce wa binciken jami’an tsaro.
Wata sanarwar da kakakin hukumar NDLEA Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi ta ce an kama wadda ake zargin ne ranar Litinin 6 ga watan Yuli a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin tantance fasinjoji da suka biyo wani jirgin Qatar Airways daga Doha zuwa Abuja.
“Kodayake daga farko ta musanta tafiya da jakkunan, bayan jami’ai sun samu sun tabbatar da cewa jakkunan biyu ɗauke da miyagun ƙwayoyi na ɗauke ne da alamu da suka dace da fasfo ɗinta, ta janye maganarta kuma ta amsa cewa ita ce mai jakkunan tana mai ƙarawa da cewa ta manta cewa ita ta shigar da jakkunan,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ambato matar tana iƙirarin cewa ta yi tafiya daga Cambodia ta hanyar Doha zuwa Abuja.
“Bayanan sirrin da suka taimaka wajen kama ta sun nuna cewa mamba ce ta wata ƙungiya ta ƙasa da ƙasa ta masu safarar miyagun ƙwayoyi tare da mijinta/abokin zamanta, Jan Coenraad De Jager, wanda ke zama a Cambodia daga inda suke safarar miyagun ƙwayoyinsu a hanyar Cambodian zuwa Afirka Ta Kudu,” in ji sanarwar.














