| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Hare-haren saman sojin Nijeriya sun kashe gomman 'yanta'addan Boko Haram
Samamen da aka kai a jihar Borno ya lalata wuraren ɓuya na 'yanta'addan da raunana ikon yiwuwar sake taruwa na ƙungiyar, in ji sojin ƙasar
Hare-haren saman sojin Nijeriya sun kashe gomman 'yanta'addan Boko Haram
Rundunar sojin saman Nijeriya tana taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da ta'addanci a ƙasar

Gomman ‘yanta’addan Boko Haram ne aka kashe ranar Asabar a wani jerin hare-haren sama da aka kai kan wuraren ɓuyar ƙungiyar a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, in ji rundunar sojin saman ƙasar.

Mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar Ehimen Ejodame ya bayyana hakan ne a wata sanarwa inda ya bayyana cewa an ƙaddamar da samamen ne a yankin Yaganari.

Ejodame ya ce gomman ‘yanta’adda ne aka kashe yayin da saura suka tsere da raunuka.

Ya ce an lalata wuraren ɓuyan ‘yanta’adda a hari saman yana mai ƙarawa da cewa an ƙwace bamaba-bamai da aka haɗa da hannu da makamai masu yawa a lokacin samamen.

"Kafin a kai hare-kare kan wuraren, bayanan da aka tattara ta sama sun tabbatar da cewa akwai kayayyakin ‘yanta’adda da cibiyoyin sufurinsu a wurin," in ji Ejodame.

Ya bayyana aikin a matsayin wata muhimmiyar nasara cikin yaƙin da ake yi da ta’addanci, yana mai cewa lamarin ya ƙara raunana ikon ‘yanta’addan na iya taruwa da kuma tafiya yadda suke so.

Tun farkon shekarun 2000 ne Boko Haram ta fara aika-aika. Gomman dubban mutane ne aka kashe a hare-haren ta’addanci da ƙungiyar ta ƙaddamar tun shekarar 2009.

Tun shekarar 2015, ƙungiyar ta kuma ƙaddamar da hare-hare kan ƙasashe maƙwabta, Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar. An kashe aƙalla mutum 2,000 a hare-haren Boko Haram a faɗin tafkin Chadi.

Ɗaruruwan dubban mutane ne hare-haren ta’addanci da tashe-tashen hankali suka raba da muhallinsu a yankin.

Rumbun Labarai
Matatar mai ta Dangote ta fara dakon fetur kyauta zuwa wasu jihohin Nijeriya
Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci a soke shirin gyaran hali na tubabbun 'yan Boko Haram
Jihar Legas ta kama mabarata 396, tana tantance bayanansu domin mayar da su jihohinsu na asali
Nijeriya za ta binciki manyan kamfanonin fasaha kan amfani da labaran ƙasar ba bisa ƙa’ida ba
Gwamnatin Nijeriya ta bai wa 'yan ƙasarta damar ƙarshe ta kwashe su daga Afirka ta Kudu
‘Yansandan Nijeriya sun dakile harin ‘yanbindiga a Sokoto
Yadda matsalar tsaron Nijeriya ke ƙara barazana ga wadatar abinci
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da fara ayyukan Bama zuwa Banki da Dikwa zuwa Gamboru-Ngala
Hukumar INEC ta Nijeriya ta tsawaita aikin rajistar masu zaɓe da makwanni biyu
Kotu ta samu mutum biyu da laifin ta'addanci a Nijeriya
Nijeriya ta ƙaddamar da masana'antar sarrafa lithium mafi girma a Yammacin Afirka a jihar Nassarawa
Amurka ta janye akasarin sojojinta da ta aika Nijeriya
Yunwa ta kai mummunan mataki da bai taɓa kai wa ba a shekaru 10 a Arewacin Nijeriya - WFP
Sojojin Nijeriya sun kashe ’yanta’adda 662, sun ceto 951 da aka sace cikin watanni uku
CBN ya soke lasisin ƙananan bankuna na Microfinance 46 saboda rashin cika ƙa’idoji
Nijeriya ta yi alƙawarin tallafa wa 'yan ƙasar 271 da suka dawo daga Afirka ta Kudu
Ɗan Nijeriya ya mutu bayan sakinsa daga kurkuku a Côte d'Ivoire
Gwamnatin Nijeriya ta karɓi 'yan ƙasar 269 da aka sake mayarwa gida daga Afirka ta Kudu
Jam'iyyar adawa ta NDC a Nijeriya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu game da rajistarta
Sojojin Nijeriya sun ceto ɗalibai da malaman GDSS Lassa 10 a Jihar Borno