Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan 17 ne suke fuskantar matsananciyar yunwa a faɗin jihohin arewacin ƙasar tara, tana mai gargaɗin cewa rikici da janye tallafi na sa wa matsalar abinci ta yi munin da ba ta taɓa kai wa ba a kusan shekaru 10 da suka gabata.
Nazari na baya bayan nan a kan matsalar ƙarancin abincin ya nuna yawan mutanen da ke fusknatar matsalar, da yanayin gaggawa da ake ciki da yadda waɗanda ke cikin matsananciyar yunwa suka ƙaru da kusan miliyan biyu idan aka kwatanta da hasashen da aka yi na baya, in ji hukumar ta WFP a wata sanarwa.
Binciken ya fayyace zurfin yanayin jinƙai da matsalar tsaro ke jawowa a ƙasar ta Afirka mafi yawan al’umma, inda ‘yanta’adda a arewacin ƙasar suka tarwatsa al’ummomi, da hana manoma ayyukan gona tare da hana shigar da agaji.
Rikicin yana ƙara muni a lokacin damina, inda iyalai ke rasa abinci a rumbunansu kafin lokacin girbi.
WFP ta ce, Jihar Borno, wadda ita ce cibiyar da ‘yanta’adda suke cin karensu babu babbaka, na da fiye da mutum miliyan uku da ke fama da matsanancin rashin abinci, da suka haɗa da fiye da mutum 750,000 da ke fuskantar mummunar yunwa.
“Idan mutane suka rasa hanyar samun abinci, aka raba su da muhallansu, to rashin tabbas na ƙaruwa,” in ji daraktan Afirka ta WFP da Afirka ta Tsakiya Kinday Samba, yana mai cewa rikici yana yaɗuwa a faɗin yankin da tilasta wa mutane barin gonakinsu.
WFP ta ce a yanzu za ta iya taimakon mutane kadan ne kawai daga miliyan 1.3 da ta taimaka wa bara a jihohin arewa maso gabashin ƙasar guda uku, inda mutum miliyan 6.2 ke fuskantar rashin abinci.
Hukumar ta ce tana buƙatar dala miliyan 89 nan da wata shida don tabbatar da cigaba da samun abinci da sauran abubuwan buƙata a faɗin arewacin Nijeriya.











