| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Kotu ta samu mutum biyu da laifin ta'addanci a Nijeriya
Rundunar 'yansandan ƙasar ta ce an fara sharia'r mai alaƙa da ta'adanci ne a jihar Katsina bayan an kama mutanen a wani babban samame kan safarar makamai a watan Satumbar 2025.
Kotu ta samu mutum biyu da laifin ta'addanci a Nijeriya
TSOHON HOTO: Wannan ba shi ne karon farko da kotu ta samu mutane da laifi kan ta'addanci a Nijeriya ba a cikin wannan shekarar / Reuters

Wata babbar kotun tarayyar Nijeriya a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar ta ɗaure mutum biyu bayan ta same su da laifuka masu alaƙa da ta’addanci.

Wata sanarwar da rundunar ‘yansandan ƙasar ta fitar da sa hannun kakakin rundunar na ƙasa, CSP Anietie Okokon Edem Iniedu, ta ce an fara sharia’r ne bayan rundunar ta kai wani babban samame kan safarar makamai a watan Satumbar shekarar 2025.

“Idan za a iya tunawa jami’an rundunar ‘yansandan jihar Katsina sun kama waɗanda ake zargi, Abdussalam Muhammad da Aminu Mamman, a kan hanyar Ingawa zuwa Karkarku, a jihar Katsina, yayin da suke safarar wasu bindigogi da aka haramta domin kai wa masu aikata laifuka,” in ji sanarwar.

“Abubuwan da aka ƙwace a samane sun haɗa da bindiga mai jigida samfurin PKT ɗaya da harsasai 230 na PKT da harsasai1,663 masu girmam milimita 7.62mm da milimita 39mm da harsasan bindigar AK-47, da kuma motocin da ake amfani da su wajen safararsu, acewar CSP Anietie.

Bayan cikakken bincike, an gurfanar da waɗanda ake zargin gaban wata babbar kotun tarayya da ke Katsina bisa tuhume-tuhume biyar da suka haɗa da haɗa baki don aikata laifi da riƙe tare da safarar haramtattun makamai ba bisa ƙa’ida, in ji sanarwar.

Kazalika a cikin tuhume-tuhumen akwai taimaka wa ‘yanta’adda da kuma shirin ta’addanci, wani aikin da ya saɓa wa tanade-tanaden dokar haramta ta’addanci ta shekarar 2022, a cewar sanarwar.

“Bayan cikakken shari’ah inda masu gabatar da ƙara suka gabatar da shaidu da kuma hujjoji a rubuce da hujjoji na kayayyaki, an sami dukkan waɗanda ake zargin da laifi kan dukkan tuhume-tuhumen,” in ji sanarwar.

“Daga baya kotun ta yi wa ko wanne daga cikin waɗanda aka samu da alifin ɗaurin shekara biyar a kan tuhuma ta farko da kuma ɗaurin shekara ashirin a kan ko wace tuhuma daga ta biyu zuwa ta biyar,” in ji kakakin rundunar ‘yansandan.

Yayin da Nijeriya ke fama da matsaloli na tsaro daga ‘yanbindiga da ‘yanta’adda, ɗaya daga cikin ababen da ke ɗaure wa mutane kai shi ne ta yadda masu tayar da ƙayar bayan suke samun makamai da suke aikata laifuka da su.