Amurka ta janye yawancin dakarunta daga Nijeriya bayan harin da aka kai a watan Mayu wanda ya kashe Abu-Bilal al-Minuki, mataimaki na biyu a jagorancin ƙungiyar Daesh a yankin Tafkin Chadi.
Dagvin Anderson, kwamandan Rundunar Amurka ta Afrika (AFRICOM), ya sanar da batun janye sojojin ne a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a birnin Luanda na Angola, bayan kammala taron shugabannin hafsoshin tsaro na Afirka na shekarar 2026.
Ya ce duk da janye yawancin dakarun, Amurka za ta ci gaba da kasancewa abokiyar hulɗa da Nijeriya a fannin musayar bayanan sirri.
Da yake magana kan ƙalubalen tsaro a Afirka da kuma yadda Amurka ke tallafa wa ƙawayenta ba tare da tsoma bakin ƙasashen waje ba, kwamandan AFRICOM ya bayar da misali da aikin sojin da ya kashe Al-Minuki.

Amurka ta tura kusan jami’an soji 200 zuwa Nijeriya a watan Fabrairu domin tallafa wa ayyukan tattara bayanan sirri, sa ido da kuma yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.
Aikin tura dakarun ya zo ne a daidai lokacin da haɗin gwiwar tsaro tsakanin Washington da Abuja ke ƙara ƙarfi wajen yaƙi da Daesh da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a yankin.
An tura dakarun ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake sa wa ido kan batun ‘yancin addini, inda ya yi alƙawarin ƙara tallafin Amurka wajen yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a ƙasar.
A ranar 25 ga Disamban 2025, Amurka ta kai hare-haren sama kan sansanonin ’yanta’adda guda biyu da ke cikin dajin Bauni a ƙaramar hukumar Tangaza ta Jihar Sokoto.
Haɗin gwiwar ya kai ga kashe Abu-Bilal Al-Minuki, mataimaki na biyu a jagorancin ƙungiyar Daesh, a maboyarsa da ke Jihar Borno.










