| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun ceto ɗalibai da malaman GDSS Lassa 10 a Jihar Borno
Sun yi ta buɗe wuta , inda suka kashe malami ɗaya da kuma ji wa wasu mutane ciwo kafin su yi garkuwa da wasu ɗalibai da ba a san adadinsu ba
Sojojin Nijeriya sun ceto ɗalibai da malaman GDSS Lassa 10 a Jihar Borno
Sojojin Nijeriya / Nigerian army

Rundunar Operatin Hadin kai da ke yaƙar ta’addanci a arewa maso gabashin Nijeriya ta ce ta ceto ɗalibai da malamai 10 daga cikin waɗanda Boko Haram ta sace daga makaranatar GDSS Lassa ta ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno.

Sanarwar da muƙaddashin jami’in watsa labarai na rundunar, Keftin Mohammad Goni, ya fitar ta ce sojojin sun nufi inda ‘yanta’addan suka yi ne da zaran sun sami labarin harin da suka kai makarantar.

Ta ƙara da cewa sojojin sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ‘yanta’addan yayin da soja ɗaya da ɗan sa kai suka rasa rayukansu yayin arangamar da suka yi kusa da yankin Daggu.  

Kazalika sanarwar ta ce jami’an tsaron sun ƙwace baburan ‘yantadaddan bakwai yayin arangamar.

Sanarwar ‘yansanda

Daga farko dai rundunar ‘yansandan Nijeriya ta ƙaddamar da aikin neman wasu ɗailbai da ‘yantaddan Boko Haram suka sace su yayin da suke rubuta jarabawarsu ta kammala karatun sakandare (NECO) a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar ranar Litinin.

‘Yanta’addan na Boko Haram sun isa makarantar gwamnati ta GDSS da ke Lassa, a ƙaramar hukumar Askira/Uba sanye da kayan sojin boge da kuma kayayyakin jami’an tsaron daji, domin yaudarar mutane cewa su jami’an tsaro ne, kamar yadda ‘yansanda da mazauna wurin suka sanar da kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Sun buɗe wuta, inda suka kashe malami ɗaya da kuma ji wa wasu mutane ciwo kafin su sace ɗaliban da ba a san adadinsu ba.

‘Yanta’addan riƙe da muggan makamai sun danna cikin makarantar ne da safiya , inda suka yi ta harbi kafin su tafi da ɗaliban.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Borno Nahum Daso ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa an tura jami’an tsaro domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su da kuma kamo maharan.

“Da misalin ƙarfe 9 na safe (na ƙasar), ‘yantadda sun kai hari makarantar sakandare ta jeka ka dawo ta Lassa. Sun yi ta harbi nan da can. An saci ɗalibai da dama ,” kamar yadda Daso ya shaida wa Anadolu ta waya.

Ya ƙara da cewa dakarun tsaro sun yi arangama da maharan kuma kwamishinan ‘yansanda ya nemi kwamandan ‘yansanda na yankin ya jagoranci aikin da ake yi a yanzu.

“A halin yanzu suna neman ceto waɗanda aka yi garkuwa da su,” a cewar Daso, ba tare da ba da haƙiƙanin adadin ɗaliban ba.

Garkuwa da mutane na baya-bayan nan ya faru ne cikin rashin tsaro da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a arewa maso gabashin ƙasar duk da shekaru da aka shafe na ayyukan soji a kan Boko Haram da ɓangaren da ya ɓalle daga gareta, ISWAP.

Ƙungiyoyin ‘yantadda sun yi ta kai hare-hare kan makaranti a yankin arewacin ƙasar , lamarin da ke haddasa garkuwa da mutane da yawa irin na ƙaurin sunan da suka yi wajen garkuwa da ‘yanmatan Chibok a shekarar 2014 a jihar Borno.

Harin na ranar Litinin na zuwa ne makonni bayan ‘yanta’adda sun yi garkuwa da fiye da ɗalibai da malamai 40 daga makaranti uku a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo dake kudu maso yammacin ƙasar .

Lamarin ya haddasa zanga-zangar ƙungiyoyin ƙwadago da masu fafatukar kare haƙƙin bil’adama da ɗalibai a faɗin ƙasar da kuma sabunta damuwa game da amincin makaranti a faɗin Nijeriya.