| Hausa
AFIRKA
5 minti karatu
Afirka ta sami tallafin $900m domin faɗaɗa fasahar girki na zamani mara gurɓata muhalli
Tallafin ya fito ne daga haɗakar gwamnatocin duniya, masu zuba jari na kamfanoni masu zaman kansu, da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa masu fafutukar raya ƙasa.
Afirka ta sami tallafin $900m domin faɗaɗa fasahar girki na zamani mara gurɓata muhalli
Wannan tallafi na dala miliyan 900 ya fito ne daga haɗakar gwamnatocin duniya, masu zuba jari na kamfanoni masu zaman kansu

Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta bayyana cewa ƙasashen Afirka sun samu sabbin alƙawuran tallafin kuɗi da suka kai dala miliyan 900 domin faɗaɗa damar yin amfani da fasahohin girki na zamani masu tsafta, waɗanda ke maye gurbin gurɓatattun abubuwan rura wuta.

Wannan tallafi na dala miliyan 900 ya fito ne daga haɗakar gwamnatocin duniya, masu zuba jari na kamfanoni masu zaman kansu, da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na raya ƙasa. An samu nasarar samun tallafin ne ta hanyar ƙoƙarin da Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta jagoranta, ƙarƙashin haɗin gwiwar shugabanni daga ƙasashen Kenya, Norway, da kuma Amurka.

Wannan sabon alƙawari na kuɗi an ɗora shi ne a kan dala biliyan 2.2 da aka tara a taron ƙoli na farko kan Girki Mara Gurɓata Muhalli a Afirka (Africa Clean Cooking Summit) da aka yi a birnin Paris a shekarar 2024, wanda hakan ya sanya jimillar alƙawuran kuɗaɗen da aka ɗauka sun haura dala biliyan 3.1.

Za a yi amfani da waɗannan kuɗaɗe ne wajen faɗaɗa damar samun kayan rura wuta na girki waɗanda ba sa gurbata muhalli, kasko da sauran abubuwan more rayuwa masu alaƙa da hakan a fadin nahiyar.

An sanar da wannan tallafi ne yayin wani taron tattaunawa na kafar intanet kan dabarun girki mai tsafta a Afirka wanda IEA da kasar Kenya suka shirya, inda shugabanni suka duba irin ci gaban da aka samu tun bayan taron karshe, sannan suka tsara abubuwan da za a ba wa fifiko kafin babban taron na gaba da za a yi a karshen wannan shekara.

Samun damar yin girki mara gurbata muhalli
Kusan mutane biliyan 1 a fadin Afirka har yanzu ba su da damar yin girki ba tare da sun gurbata muhalli ba, inda a maimakon haka suke dogaro da gawayi, itace, da sauran kayan ruruta wuta masu gurbata muhalli wadanda hukumar IEA ta ce suna taimakawa wajen mutuwar mutane kusan 850,000 kafin lokacinsu a kowace shekara.

Taron ya hada da Shugaban kasar Kenya, William Ruto; Firaministan kasar Norway, Jonas Gahr Store; Sakatariyar Makamashi ta Amurka, Chris Wright; Kwamishiniyar Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) mai kula da Abubuwan More Rayuwa da Makamashi, Lerato Mataboge; da kuma Babban Daraktan IEA, Fatih Birol, da dai sauransu.

Girki mara gurbata muhalli yana nufin yin amfani da fasahohi da kayan ruruta wuta masu fitar da hayaki kadan, kamar su sinadarin ‘ethanol’, iskar gas ta ‘biogas’, da wutar lantarki, a maimakon tsofaffin hanyoyin girki kamar gawayi da itace. Wannan sauyi yana rage gurbatar iska mai cutarwa a cikin gida, sannan yana inganta yanayin lafiya ga miliyoyin gidaje a Afirka.

“Samun damar yin girki mara gurbata muhalli yana daya daga cikin kalubale mafi tasiri amma kuma wanda aka fi kau da kai a zamaninmu,” in ji Wright, inda ta kara da cewa hakan yana shafar rayuwar biliyoyin mutane kai-tsaye, musamman mata da yara.

Kalubalen samun kudade

Shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya bayyana cewa samun kudaden gudanarwa shi ne babban cikas wajen cimma burin samar da damar yin girki mara gurbata muhalli ga kowa da kowa a fadin Afirka. “Burin zuciya kadai ba zai wadatar ba. Dole ne a mara masa baya ta hanyar zuba jari,” in ji shi.

Shi kuwa Birol ya bayyana cewa binciken baya-bayan nan na hukumar IEA ya nuna cewa tuni aka rarraba dalar Amurka miliyan 740, wato kusan kashi daya bisa uku na alkawuran kudaden da aka sanar a Paris, a cikin kasashen Afirka guda 22.

“Wannan karin alkawari na dalar Amurka miliyan 900 yana nuna yadda yunkurin ke samun tagomashi, kuma ana sa ran samun kari kafin taron koli na gaba,” in ji Birol.

Hukumar ta IEA ta kuma fitar da wani rahoto da ke nuna cewa gwamnatoci sun fito da sabbin manufofi guda 121 na girki mara gurbata muhalli a cikin kasashen Afirka fiye da 30 tun bayan taron koli na Paris. Wadannan kasashe sun kunshi kusan kashi 80 cikin dari na al’ummar Afirka da ba su da damar yin girki ba tare da gurbata muhalli ba.

Manufofin girki mara gurbata muhalli

Hukumar ta ce tana aiki tare da Kungiyar Tarayyar Afirka domin taimaka wa gwamnatoci wajen karfafa manufofin girki mara gurbata muhalli na fadin kasa, a karkashin wani tsari da dabarun aiki na fadin nahiyar kafin taron koli na gaba.

Ta kuma kaddamar da wani sabon shiri na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu mai suna “Clean Cooking Security Programme”wanda ke da nufin karfafa hanyoyin samar da kayan girki na duniya, musamman iskar gas wato (Liquefied Petroleum Gas LPG).

Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan tasgaro da aka samu a harkar jigilar kayayyaki ta Mashigar Tekun Hormuz a farkon wannan shekara, lamarin da ya shafi kusan kashi 30 cikin ɗari na iskar gas da ake kasuwancinta a duniya.

Fiye da mutane biliyan 3.4 a faɗin duniya sun dogara ne ga iskar gas a matsayin babbar hanyar da suke dogaro da ita wajen girkinsu.

Wannan shiri zai ba da agajin ƙwararru ga ƙasashen da ke neman inganta tsaron kayan girke-girke, tare da binciko hanyoyin karfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa kan hanyoyin samar da kayan girki mara gurɓata muhalli.