Shugabannin ƙasashen mambobin ƙungiyar tsaro ta NATO suna taruwa a babban birnin Turkiyya, Ankara, domin halartar taron ƙoli na 36 na ƙungiyar. Turkiyya ba wai karɓar baƙi kawai take ba, tana ƙara bayyana muhimmin matsayinta a fannin tsaro da diflomasiyyar duniya.
Taron na kwanaki biyu yana gudana ne a lokacin da duniya ke fuskantar ƙalubalen siyasa da tsaro da suka haɗa da yaƙin Rasha da Ukraine, rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya, da kuma sabuwar muhawara kan yadda ƙasashen NATO za su raba nauyin tsaro tsakaninsu.
Baya ga zaman tarurrukan NATO, Ankara za ta kuma karɓi muhimman zaman ganawa tsakanin shugabannin ƙasashe, waɗanda ake sa ran za su yi tasiri kan makomar diflomasiyyar yanki da ma ta duniya.
Erdogan da Rutte sun tattauna gabanin taron
Bayan isowarsa Ankara ranar Litinin, Sakatare Janar na NATO, Mark Rutte ya gana da Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a Fadar Shugaban Ƙasa, domin duba ajandar taron da kuma tattauna halin da ake ciki a yankunan da ma a duniya.
Shugaba Erdogan ya ce Turkiyya ta kammala duk shirye-shiryen taron, yana mai bayyana fatan cewa haɗuwar za ta haifar da sakamako mai kyau ga ƙungiyar.
Ya kuma jaddada cewa ya kamata tattaunawar ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen NATO wajen bunƙasa masana'antun tsaro. Kuma a cewarsa, ƙarfin masana'antun tsaro na ƙungiyar na ƙara zama muhimmi kamar ƙarfin soji.
Masana'antun tsaro sun zama jigon taron
Ɗaya daga cikin manyan batutuwan taron shi ne bunƙasa masana'antun tsaro, kuma tun kafin fara babban taron shugabannin, wakilan ƙasashe sun fara halartar Dandalin Masana'antar Tsaro na NATO da ake gudanarwa a Ankara.
Suna amfani da danadalin wajen sanar da sababbin tsare-tsaren saka hannun-jari da haɗin-gwiwar masana'antu, domin ƙarfafa ƙarfin kariyar NATO na dogon lokaci.
Ministar Tsaron Netherlands, Dilan Yesilgöz, ta sanar da cewa ƙasarta za ta ƙaddamar da sababbin ayyukan tsaro da sayen kayan aiki da darajarsu ta haura Euro biliyan uku.
Shirin ya haɗa da haɗin gwiwar kariyar sararin samaniya da Belgium, da kuma shirye-shiryen jiragen ruwa tare da Birtaniya.
Ta ce, "Muna buƙatar junanmu domin tabbatar da tsaro," tana mai cewa ya kamata Turai ta ci gaba da saka hannun jari a masana'antun tsaronta ba tare da la'akari da sauye-sauyen siyasa a Washington ba.
Turkiyya na son zama cibiyar ƙera kayan tsaro
Ana kuma sa ran taron zai ƙara ƙarfafa burin Turkiyya na zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ƙera kayan tsaro a duniya.
Jami'an ƙasar sun bayyana cewa Dandalin Masana'antar Tsaro na daga cikin manyan abubuwan da za su ba taron armashi, yayin da Erdogan ya ce ana sa ran zai jawo hankalin ƙasashe da dama.
Farfesa Mehmet Ozkan na Cibiyar Nazarin Yaƙi ta Jami'ar Tsaron Ƙasa ta Turkiyya, ya ce, yayin da NATO ke ƙara mayar da hankali kan samar da kayan tsaro, hanyoyin samar da kayayyaki da kuma juriyar masana'antu, ƙarfin masana'antun tsaro na Turkiyya ya zama wata babbar kadara ga ƙungiyar.
Ya ce rawar Turkiyya ba ta tsaya ga matsayinta na ƙasa mai muhimmanci a yanki kawai ba, har ma tana taimaka wa NATO wajen gina sabon tsarin masana'antun tsaro.
Diflomasiyya za ta mamaye taron
Baya ga batun tsaro, ana sa ran diflomasiyya za ta mamaye batutuwan gefen taron. Masanin harkokin waje na Majalisar Tarayyar Turai, Marian Duris, ya ce muhimmancin taron Ankara ya wuce batun kashe kuɗaɗen tsaro kawai.
A cewarsa, tsaro ya kamata ya haɗa da matsayin ƙasa, ƙarfin masana'antu, da kuma tantance ainihin barazanar da ake fuskanta.
Ya ce kasancewar Turkiyya a tsakanin Turai, Bahar Maliya, Tekun Bahar Rum, da Gabas ta Tsakiya, ya sa take da muhimmanci sosai a fannoni daban-daban na tsaro.
Ganawar Erdogan da Trump
Ana sa ran Shugaba Erdogan zai gudanar da ganawa da shugabannin ƙasashen NATO da dama, ciki har da Shugaban Amurka, Donald Trump, domin ƙarfafa alaƙar Turkiyya da Amurka.
Ana sa ran za su tattauna haɗin gwiwa kan tsaro, matsalolin yanki, da kuma batutuwan sayen kayan tsaro da haɗin-gwiwar masana'antu.
Shi ma shugaba Trump zai gana da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, inda za su tattauna makomar tallafin soji ga Ukraine, yiwuwar zaman diflomasiyya da Rasha, da sauran batutuwan tsaron yanki.
Haka kuma ana sa ran Trump zai gana da Shugaban Siriya, Ahmad al Sharaa, abin da ke nuna yadda rikicin Siriya da Gabas ta Tsakiya ke ƙara zama wani muhimmin ɓangare na ajandar tsaron NATO bayan rikicin baya-bayan nan da Iran.
Saƙon Washington
Baya ga Fadar White House, taron ya kuma samu halartar tawagar 'yan Majalisar Dokokin Amurka daga jam'iyyu biyu, ƙarƙashin jagorancin Sanata Jeanne Shaheen.
Tawagar za ta halarci taron da kuma Dandalin Masana'antar Tsaro, domin nuna goyon bayan Majalisar Dokokin Amurka ga NATO da Ukraine.
Ana sa ran za su ƙarfafa ƙawayen NATO su ci gaba da ƙara kashe kuɗi kan tsaro, tare da tabbatar da cewa batun Ukraine ya ci gaba da kasancewa cikin manyan abubuwan da ƙungiyar ke mayar da hankali a kai.
Taron da zai haɗa duniya
Mataimakin Shugaban Turkiyya, Cevdet Yilmaz, ya bayyana taron a matsayin na tarihi, yana mai cewa ana gudanar da shi ne a wani lokaci mai matuƙar muhimmanci da duniya ke fuskantar manyan sauye-sauye.
Baya ga shugabannin dukkan ƙasashe 32 na NATO, Ankara ta kuma karɓi baƙi daga ƙasashen Indo-Pacific, Tarayyar Turai, da kuma Ƙungiyar Istanbul Cooperation Initiative, abin da ke nuna yadda NATO ke ƙara faɗaɗa haɗin-gwiwarta sama da yankin Turai da Arewacin Amurka.
Muhimman shawarwari daga tattaunawar sirri
Ko da yake za a sanar da hukuncin taron ne bayan zaman Majalisar Arewacin Atalantika ranar Laraba, ana ganin wasu daga cikin mafi muhimmancin cigaban da za a samu za su fito ne daga tattaunawar sirri tsakanin shugabannin ƙasashe.
Yayin da shugabannin ke tattauna yaƙe-yaƙen Ukraine da na Gabas ta Tsakiya, makomar tsaron ƙasashen Atalantika da kuma bunƙasar haɗin-gwiwar masana'antun tsaro, Ankara ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin diflomasiyyar duniya a wannan mako.
Ana sa ran taron zai nuna cewa makomar NATO ba za ta dogara ga kashe kuɗin tsaro da ƙarfin soji kaɗai ba, har ma da diflomasiyya, ƙarfin masana'antu, da kuma sauye-sauyen siyasa da tsaro da suka wuce iyakokin Turai.










