| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Mai tsaron bayan Argentina ya ce alƙalan wasan Gasar Kofin Duniya 'na aiki mai kyau'
"Mun damu ne kawai da yin iya ƙoƙarinmu a cikin fili," in ji mai tsaron baya Lisandro Martinez bayan ce-ce-ku-cen Masar.
Mai tsaron bayan Argentina ya ce alƙalan wasan Gasar Kofin Duniya 'na aiki mai kyau'
"Kamar ka da yaushe, Abin da ya bambanta wanna tawaga shi ne girmama abokan gaba," a cewar Martinez. (Toshon Hoto)

Mai tsaron bayan Argentina Lisandro Martinez ya yi watsi da ce-ce-ku-ce game da alƙalanci a Gasar Kofin Duniya kuma ya ce jami’an wasa suna aiki mai kyau bayan Masar ta soki hukunce-hukuncen a kayen da ta sha da ci 3-2 a wasansu na zagayen ƙasashe 16.

Argentina ta kai matakin takwas na ƙarshe bayan ta taso daga kasancewa ƙasa da ƙwallaye biyu kuma ta samu ta doke Masar cikin mintuna 11.

Sai dai kuma wasan ya tayar da ƙorafi daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Masar game da amfani da VAR, musamman yadda aka soke ƙwallon da Mostafa Zico ya zura a raga minti 62 da fara wasa.

Argentina ta fuskanci suka mai tsauri a shafukan intanet, inda mutane da yawa ke iƙirain cewa ƙasar mai kare kambunta tana amfana da sonkai daga alƙalan wasa masu hura wasanni.

Shugaban ɓangaren alƙalanci na FIFA Pierluigi Collina ya kare jami’an, inda ya yi watsi da zarge-zargen sonkai kuma ya jaddada cewa alƙalan suna aiki ne bisa ‘yancin kansu.

"A a, babu komai," kamar yadda Martinez ya shaida wa manema labarai lokacin da aka tambaye shi kan ko yana da wani abin faɗa game da alƙalanci a gasar.

"Ina tunanin suna aiki mai kyau. Wannan wani abu ne gare ku (kafafan watsa labarai), waɗanda a wasu lokuta ke tayar da ce-ce-ku-ce. Mun mayar da hankalinmu ne kan yin iya ƙoƙarinmu a cikin fili kawai," in ji shi .

Karawa da Switzerland

Argentina za ta kara da Switzerland ranar Asabar a wasansu na kwata final a Kansas City, inda ƙasa mai kare kambunta ke bayyana girmamawa ga ƙasar ta Turai yayin da take jaddada buƙatar da ke akwai ta mayar da hankali kan ƙwarewarta.

"Kamar kullum, abin da ya bambanta wannan tawaga shi ne girmama abokan gaba," in ji Martinez.

"Idan Switzerland suka kasance a wannan matakin , hakan ya faru ne saboda suna da ƙwarewa da yawa. Mun kalli wasansu da Colombia, kuma suna ƙoƙarin wasa a ko wane lokaci. Suna da ƙarfi sosai a zahiri da kuma wajen raba ƙwallaye. Ina ganin zai kasance babban wasa saboda tawagogin biyu suna ƙoƙarin wasa."

Mai tsaron gida Cristian Romero ya maimaita saƙon, yana mai cewa Argentina tana mayar da hankali ne kawai kan gyara kurakuranta.

"Koma da wane ne muka haɗu, ko ma mene ne sunan abokan hamayyar ko kuma inda suka fito, muna mayar da hankalinmu ne kan gyara kurakuran da muke da su," in ji Romero, wanda ya zura ƙwallon Argentina na farko a ragar Masar.

Rumbun Labarai
CIA ta yi shakkar iƙirarin da Isra'ila ta yi kan shirin halaka Trump bayan taron NATO: rahoto
Za a fara shari'ar wanda ake zargi da hannu a kashe Tupac Shakur a Amurka
‘Yan Bangladesh akalla 16 sun mutu sakamakon gobara a masana'antar yin kujeru ta Saudiyya
Gobarar daji a jihar Washington ta Amurka ta tilasta wa dubban mutane tserewa
Jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi kusa da wani sansanin soji
Tarayyar Turai ta yi kira da a zartar da umarnin Kotun ICC na kamo Netanyahu
Macron ya ce Faransa na fama da gobarar daji mafi muni da ba a taɓa ganin irinta ba
Turai na babbakewa: Me muka sani zuwa yanzu?
Faransa da Sifaniya na fama da mummunar gobarar daji
Yadda kujerar Firaministan Birtaniya ke komawa tamkar kujerar aski
Trump ya ce ba za a yi yarjejeniyar nukiliya da Saudiyya ba sai ta amince da gyara alaƙa da Isra'ila
Trump ya tarbi gawawwakin sojojin Amurka da aka kashe a yaƙin Iran
Trump ya amince da yarjejeniyar shirin nukiliya na farar-hula da Saudiyya — Rahoto
Sabon Firaministan Birtaniya Burnham ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa
Netanyahu ya fusata Trump bayan ya caccaki shirin Amurka na sayar wa Turkiyya F-35: Rahoto
Ana fargabar mutuwar 'yan ƙabilar Rohingya fiye da 500 bayan kifewar jiragen ruwa a gaɓar Myanmar
Masu ceton dabbobi na taimaka wa tsuntsaye tsira daga bazara mai zafi
Ƙirkirarriyar Basira, ƙarfin intent da ƙa’idojin aikin jarida
Yawan masu kamuwa da cutar kansa na iya kusan ninkuwa nan da shekarar 2050
An kona gini mai kama da masallaci a Arewacin Ireland  a yayin da ‘yansanda ke gudanar da bincike