| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi kusa da wani sansanin soji
An garzaya da matuƙin jirgin wani asibiti "domin duba lafiyarsa da kuma yi masa magani na raunukan da ya ji da ba sa barazana ga rayuwa," in ji jami'ai.
Jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi kusa da wani sansanin soji
Jami'ai na kashe wutar da ke cin wani jirgin yaƙin F-35 da ya faɗi kusa da titin sauƙar jirgin sama na sojin ƙasar da ke a San Diego, California

Wani jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi a kusa da wani sansanin soji a San Diego, amma matuƙin jirgin ya samu ya kuɓutar da kansa kafin jirgin ya kai ƙasa, a cewar jami’ai.

"An samu wani hatsarin jirgi da ya shafi wani jirgin sojojin ruwan Amurka [samfurin] F-35B a cikin harabar" filin jirargen saman sojin ruwa na Miramar da misalin ƙarfe 10:00 na safe (ƙarfe 1700 agogon GMT), kamar yadda wani mai magana da yawun sojin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.

"An fitar da matuƙin jirgin kuma an samo shi."

Wata sanarwar da aka fitar daga baya daga sansanin sojin ta ce an kai matuƙin jirgin wani asibiti "cikin wani yanayi na daidaito domin duba lafiyarsa da kuma yi masa magani na raunuka da ba sa barazana ga rayuwarsa."

Bidiyon da aka yayata a shafukan sada zumunta sun nuna hayaƙi na tashi sama daga jirgin saman, a yayin da aka tura ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Filin jiragen sama sojin ruwan (MCAS) da ke Miramar sananne ne a faɗin duniya a matsayin inda ya taɓa kasancewa gida ga makarantar horas da matuƙan jiragen yaƙi na sojin ruwan Amurka inda ake horas da manyan matuƙan jirage, wanda ya yi suna a fim ɗin shekarar 1986 mai suna "Top Gun" inda Tom Cruise ya fito a matsayin tauraro.

Ko wane jirgin F-35B, wani samfuri na jirgin yaƙi mai tafiya cikin sirri babu ƙara da ke iya tashi sama kai tsaye da kuma sauƙa kai tsaye, kudinsa ya kai kimanin dala miliyan $109, in ji Lockheed Martin mai ƙera shi.