Hukumomi a Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya sun tabbatar da cewa mutum 511 sun kamu da cutar mashaƙo kuma mutum 13 sun mutu sakamakon cutar daga watan Janairu zuwa 8 ga watan Satumba.
Kwamishinan Lafiya na Jihar, Muhammad Gana, ne ya bayyana wannan yayin da yake zanta wa da kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) a Damaturu babban birnin jihar ranar Alhamis.
Gana ya bayyana cewa mutuwar mutum 13 ta yi daidai da kashi 2.5 cikin 100 na mace-mace sakamakon cutar, mace-macen da ba su kai na sauran jihohin da lamarin ya shafa ba a faɗin ƙasar.
Ya tabbatar da cewa ɓullar cutar ta shafi ƙananan hukumomi 12 ne a faɗin jihar, kuma tuni aka soma shirye-shiryen yin rigakafi a waɗannan wuraren.
Gana ya ƙara da cewa adadin mutum 511 da suka kamu da cutar mashaƙo a yanzu bai kai 1,100 da aka ba da rahoton samu a watan Satumbar shekarar 2025 da ma shekarun baya ba.
Ya bayyana cewa raguwar da ake samu tun shekarar 2023, a lokacin da jihar ta samu adadi mafi yawa na mutum 3,080 da suka kamu da cutar, na da nasaba ne da matakin da aka ɗauka na daƙile cutar.
Matakan da kwamishinan ya ayyana sun haɗa da ba da magani kyauta ga waɗanda lamarin ya shafa da bai wa ma’aikatan lafiya horo na musamman game da dabarun daƙile cutar da zafafa rigakafi a wuraren da ke da wahalar kaiwa da wayar da kan jama’a game da cutar.
Ƙarin matakai sun haɗa da dannawa na ma’aikatan lafiya wajen bibiyar waɗanda suka haɗu da masu cutar da musayar bayanai da masu ruwa da tsaki da ganawa a-kai a-kai da kuma tattaro kayayyakin aiki domin fuskantar ɓullar cutar.
Gana ya yaba wa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Asusun Kula da ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF da ƙungiyar horas da ma’aikatan lafiya yaƙar yaɗuwar cututtuka a Afirka (AFENET) wajen tallafa wa aikin rigakafin jihar kan cutar mashaƙo, musamman a rugagen makiyaya.
Cutar mashaƙo cuta ce ta da ƙwayoyin halittu ke yaɗawa wadda ke shafar maƙwogwaro da kuma sama-saman hanyar numfashi.
Cutar ta fi yaɗuwa ne ta hanyar ƙananan abubuwan da ke fitowa ta hanyar tari ko atisahwa kuma wasu lokuta ta hanyar haɗuwa kai tsaye da fata mai lahani da ta kamu da cutar ko kuma gurɓatattun ababen da ke fitowa daga jikin wanda ya kamu da ita.



















