Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da dukkan ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu, tare da umartar ’yan majalisa, kwamitoci, jami’ai da ma’aikata da su ƙaurace wa ayyukan majalisa da hukumomin Afirka ta Kudu suka shirya ko suka karɓi baƙuncinsu.
Matakin ya biyo bayan ƙara samun damuwa kan rahotannin hare-haren ƙabilanci, ciki har da kashe ’yan Nijeriya da korarsu daga muhallansu, lalata kadarori da kuma tsoratar da ’yan Afirka da ke zaune a Afirka ta Kudu.
A cikin wata sanarwa da Akawun Majalisar Dokokin Ƙasa, Kamoru Ogunlana, ya saka wa hannu, shugabannin majalisar sun ce dakatarwar ta shafi tarukan ƙasa da ƙasa, tarukan horaswa, bitoci, tarukan majalisu, musayar ra’ayoyin ’yan majalisa da sauran shirye-shiryen da hukumomin majalisar Afirka ta Kudu suka shirya ko suka karɓi baƙuncinsu.
Ƙauracewar ta shafi halartar irin waɗannan shirye-shirye kai tsaye da kuma ta kafafen intanet, kuma za ta ci gaba da aiki har sai an ba da wata sanarwa ta daban.
Majalisar Dokokin Nijeriya ta ce matakin ba shi da nufin lalata dangantakar tarihi, diflomasiyya da alakar jama’a da ta jima a tsakanin Nijeriya da Afirka ta Kudu, sai dai yana nuna damuwa kan tsaro, mutunci da jin daɗin ’yan Nijeriya da ke zaune tare da gudanar da halastattun harkokin kasuwanci a ƙasar.
Ta ce an samu rahotannin cewa an kashe wasu ’yan Nijeriya, an raunata wasu, an raba wasu da muhallansu, yayin da aka tilasta wa wasu barin sana’o’insu, jarinsu, gidajensu da sauran kadarorinsu sakamakon hare-haren tashin hankali da ake kaiwa akai-akai.
Shugabannin majalisar sun kuma lura cewa duk da kiraye-kirayen da gwamnatin Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki suka yi ga hukumomin Afirka ta Kudu da su ɗauki matakan gaggawa domin kare ’yan Nijeriya da sauran baƙin ’yan ƙasa tare da gurfanar da masu aikata hare-haren ƙabilanci a gaban kotu, har yanzu ana ci gaba da samun rahotannin irin waɗannan hare-hare.
Majalisar Dokokin Nijeriya ta amince da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na taimaka wa ’yan Nijeriya da abin ya shafa da kuma sauƙaƙa kwashe ’yan Nijeriya daga Afirka ta Kudu, amma ta yi kira da a ɗauki ƙarin tsauraran matakai domin hana sake faruwar hare-haren.
Ta buƙaci gwamnatin Afirka ta Kudu da ta ɗauki matakan gaggawa domin kare ’yan Nijeriya da sauran ’yan Afirka, gudanar da cikakken bincike kan rahotannin hare-haren, kama waɗanda ake zargi da hannu tare da gurfanar da duk wanda aka tabbatar da laifinsa a gaban doka.
Shugabannin majalisar sun kuma buƙaci Majalisun Dokokin Jihohi da su lura da wannan mataki tare da yin la’akari da ɗaukar irin waɗannan matakai, yayin da suka sake jaddada aniyar majalisar na ci gaba da sa ido kan tsaro da jin daɗin ’yan Nijeriya da ke Afirka ta Kudu.
















