| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
INEC za ta ƙaddamar da na’urar bibiyar shirye-shiryen zaɓe kai-tsaye
Shugaban hukumar, Farfesa Samuel Amupitan ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Legas, yayin wani taron bita na musamman da aka shirya wa Sakatarorin Gudanarwa na hukumar.
INEC za ta ƙaddamar da na’urar bibiyar shirye-shiryen zaɓe kai-tsaye
A watan Janairun 2027 ne za a yi manyan zabuka a Nijeriya

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya, INEC, ta ce tana shirin ƙaddamar da wata na’ura da za ta riƙa bibiyar shirye-shiryenta kai-tsaye gabanin babban zaɓen 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Samuel Amupitan ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Legas, yayin wani taron bita na musamman da aka shirya wa Sakatarorin Gudanarwa na hukumar.

Amupitan ya ce ana sa ran taron zai samar da ingantacciyar na’urar bibiyar ayyuka ta amfani da Excel, wadda za a haɗa da dashboard ɗin Cibiyar Sa-Ido da Taimakon Zaɓe ta INEC da kuma Tsarin Ayyukan Zaɓe.

Ya ce a baya hukumar ba ta da tsarin bai-ɗaya na bibiyar nauyin ayyukan da ke kan Sakatarorin Gudanarwarta.

Shugaban INEC ya ƙara da cewa sabuwar na’urar za ta bai wa Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi, Manyan Kwamishinonin Zaɓe Masu Sa-Ido, Sakataren Hukumar da hedikwatar INEC bayanai nan take kan rarraba kayayyakin zaɓe, horar da ma’aikatan wucin-gadi da kuma matakin shirye-shiryen zaɓe a kowace jiha.

“Wannan zai ba mu damar sauyawa daga mayar da martani ga matsaloli bayan sun faru, zuwa tsarin gudanarwa mai hangen nesa da kuma ɗaukar mataki tun kafin matsala ta taso,” in ji shi.

Amupitan ya ce wannan mataki ya zo ne yayin da adadin masu rajista a rajistar masu zaɓe ta ƙasa ke dab da kai wa miliyan 100.

Taron bitar zai kuma tattauna wasu muhimman batutuwa da suka haɗa da ci gaba da rajistar masu zaɓe, harkokin sufuri da sarrafa kayayyakin zaɓe, fasahar zaɓe, inganta amfani da ma’aikatan wucin-gadi da kuma bin ƙa’idojin kuɗi.

Shugaban INEC ya ce hukumar na shirin yin amfani da nasarori da darussan da ta koya daga zaɓukan da aka gudanar a wasu jihohi ba tare da bin tsarin zaɓen ƙasa baki ɗaya ba, domin samun irin wannan inganci da nasara a duk faɗin ƙasar yayin babban zaɓen da za a fara gudanarwa a watan Janairun 2027.