| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
An manta da Raphinha da Pedri cikin 'yanwasa 30 da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or
Hakan ya ƙara ba da mamaki kasancewar an ga sunayen ‘yanwasa har daga gasar Saudi Pro League ta Saudiyya a karon farko, wato Sadio Mané na AlNassr da kuma Julián Quiñones na Al-Qadsiah.
An manta da Raphinha da Pedri cikin 'yanwasa 30 da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or
Raphinha shi ne kyaftin ɗin Barcelona a halin yanzu.

Yayin da aka saki sunayen haziƙan ‘yanwasan ƙwallo guda 30 da a cikinsu za a zaɓi wanda zai lashe babbar kyautar gwarzon ƙwallon ƙafa na duniya, Ballon d'Or a bana, masoya Barcelona sun fara gunaguni.

Babu sunan kyaftin ɗin Barca, Raphinha, da kuma ɗanwasan gaba, Pedri a jerin da ya ƙunshi wasu ‘yanwasan huɗu daban da ke buga wasa a ƙungiyar ta Sifaniya.

A Talata nan ne aka saki sunayen ‘yanwasa na rukunoni daban-daban da za a zaɓi gwarazan ‘yanƙwallo daga cikin, da masu tsaron raga, da koci-koci, da kuma ƙungiyoyi da suka yi fice a shekarar bana.

Matashin ɗanwasa Lamine Yamal, da Cubarsi da kuma Rodri, wanda a kakar bara ya buga wa Manchester City, su ne ‘yanwasan da suke buga wa Barca a yanzu. Sai kuma Ferran Torres wanda ya bar Barca ya koma Paris Saint-Germain bayan kakar bara.

Sauran shahararrun ‘yanwasan da ke jerin sun haɗa da Lionel Messi, Kylian Mbappé, Jude Bellingham, Marc Cucurella, Ousmane Dembélé, Luis Díaz, Bruno Fernandes, Erling Haaland, Harry Kane, Achraf Hakimi, Khvicha Kvaratskhelia, William Saliba, da sauransu.

Akwai dama

Masu sharhi kan ƙwallo na ganin cewa Pedri bai nuna bajinta a gasar Kofin Duniya da aka kammala a watan Yuli ba, inda Fabián ya take matsayinsa a tawagar Sifaniya wadda ta lashe kofin.

Shi ma Raphinha, wanda shi ne kyaftin ɗin Barcelona a yanzu bai nuna wata bajinta a Kofin Duniya ba, a tawagar ƙasarsa Brazil. Amma duk da haka rashin ganin sunansu duk da rawar da ya suka taka a Barca ya janyo cecekuce.

Hakan ya ƙara ba da mamaki kasancewar an ga sunayen ‘yanwasa har daga gasar Saudi Pro League ta Saudiyya, waɗanda ke bayyana a karon farko, wato Sadio Mané na AlNassr da Julián Quiñones na Al-Qadsiah.

A kakar bara, Raphinha ya buga wasanni 33 a Barcelona, ya ci ƙwallo 21 kuma ya lashe kofunan La Liga da Spanish Super Cup, kamar yadda shi ma Pedri ya lashe tare da shi.

Sai dai kuma, duk da wannan damuwa, masoya Barcelona na da kyakkyawan fatan ganin wani ɗan Barca ya lashe kyautar Ballon d'Or, kasancewar Lamine Yamal, da Rodri, wanda ya taɓa lashe kyautar a baya, suna wakiltar su.

Rumbun Labarai
Messi ya ci ƙwallonsa ta 100 a Inter Miami yayin da suka lashe Kofin Campeones
Mbappe ya ce ya ƙi sa rigar Ceuta yadda ya kamata ne don tausaya wa baƙin haure 'yan Morocco
Messi na shirin buga wa Argentina wasansa na ƙarshe
Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar
'An yi wa Arsenal fasha a wasansu da Aston Villa', in ji hukumar gasar Firimiya
NFF ta naɗa Eguavoen a matsayin kocin wucin-gadi na Super Falcons
Barcelona ta miƙa ƙoƙon-bara wajen masu zuba jari don neman kuɗin gyaran filin wasa
Turkiyya ta kuma lashe kofin gasar volleyball ta mata ta nahiyar Turai
An yanke wa Tiger Woods hukuncin haramcin tukin mota tsawon shekaru 5 saboda tuki cikin maye
Muhimman batutuwa game da ritayar Messi daga tawagar Argentina
Sakon Lionel Messi na yin ritaya daga buga kwallo a matakin kasa-da-kasa
"Jikina ya fara sakwarkwacewa" in ji Djokovic, bayan an fitar da shi daga Gasar US Open ta bana
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya Musa Gusau ya yi murabus
Ɗanwasan Kamaru Carlos Baleba ya koma Man Utd daga Brighton
Habasha ta shiga takarar ɗaukar nauyin gasar AFCON ta 2028
An sayar da ƙwallon da Maradona ya ci Ingila da hannu a kan $3.35M
Ɗan Nijeriya Semi Ajayi ya taimaka wajen yi wa Man Utd dukan wulaƙanci a farkon Gasar Firimiya
Cristiano Ronaldo ya fara kakarsa ta 25 da ƙwallonsa na 977 a tarihin wasansa