Hukumar gasar Firimiya ta Ingila ta amsa cewa alƙalan bidiyo na VAR sun tafka kuskuren alƙalanci wanda ya cutar da Arsenal, a wasan da suka kara da Aston Villa na Firimiya ranar 31 ga Agustan da ya gabata.
Wasan ya gudana ne a filin wasan Aston Villa, wato Villa Park, inda Arsenal ta yi nasara da ci 1-0.
Sai a yanzu ne wani kwamitin duba muhimman batutuwan da suka faru a wasa, Key Match Incident (KMI), ya yanke hukuncin cewa alƙalan wasa sun yi kuskuren hana Arsenal fenareti ana dab da ƙare wasan.
Ɗanwasan Villa, Ian Maatsen ne ya yi ƙoƙarin tare ƙwallo a hannun ɗanwasan Arsenal, Bruno Guimaraes, amma sai ya kwarfe ƙafar ɗanwasan kuma bai samu taɓa ƙwallon ba.
Laifin ya cancanci a ba shi jan kati sannan a ba da bugun fenareti, in ji hukumar. Amma alƙalin wasa, Jarred Gillett ya yi watsi da ƙorafin ‘yanwasan Arsenal.
Shi ma alƙalin VAR, James Bell, wanda ya duba bidiyon abin da ya faru ya aminta da hukuncin alƙalin cikin fili, wanda ya ƙona ran masoya da ‘yanwasan Arsenal duk da sun samu maki 3 daga wasan.
Hukumar gasar ta wallafa rahoton kwamitin nata a shafin intanet, inda ta jaddada cewa laifin Maatsen mummuna ne, kuma alƙalan VAR sun tafka kuskure, saboda ya kamata a ce sun bayar da fenareti.
Wannan lamari ya ƙara janyo muhawara kan amfani da alƙalin bidiyo na VAR a gasar Firimiya, wanda ke nufin kawar da kurakuran alƙalan wasa.



















