Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta kama wasu mutane biyu a jihar Adamawa da ke Arewa maso gabashin ƙasar da tsabar kuɗi har Naira miliyan 34, da ake zargin suna da alaƙa da wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane.
An kama mutanen ne a wani samame da jami’an hukumar suka gudanar a jihar, kamar yadda Konturolan Hukumar na Adamawa, Sani Sle-Jega ya bayyana ranar Laraba a wani taron manema labarai a Yola, babban birnin jihar.
Sule-Jega ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen sun yi iƙirarin cewa an tanaji kuɗin ne domin biyan kuɗin fansa don kuɓutar da ɗan’uwansu da aka yi garkuwa da shi.
Ya ce an miƙa mutanen biyu da kuɗin da aka ƙwato ga Rundunar ’Yansandan Nijeriya domin ci gaba da gudanar da bincike.
A wani samame na daban, jami’an Hukumar sun kama baƙin-haure 17 a jihar ta Adamawa da ba su da takardun izinin zama a Nijeriya.
An kama mutanen ne a wani gida mai ɗakuna uku da ke Rumde Baruwa, a ƙaramar hukumar Yola ta Arewa.
‘‘Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, 13 daga cikin mutanen ‘yan ƙasar Kamaru ne, maza takwas da mata biyar, yayin da sauran mutum huɗu kuma ’yan ƙasar Chadi ne, dukkansu maza,’’ a cewar Sule-Jega.
Ya ce hukumar ta lura da irin sauyin salon da baƙin-haure waɗanda ke zama a Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba suke bi wajen samun masauki, inda suke ƙara amfani da gidaje masu zaman kansu da ba a yi musu rajista ba maimakon otal-otal.
Konturolan ya ce hukumar na ƙara tsaurara matakan sa ido da kuma amfani da bayanan sirri wajen gano sabbin hanyoyin da baƙin-haure ke bi wajen shiga da kuma zama ba bisa ƙa’ida ba a jihar.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani sahihan bayanai da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.






















