| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin kafa rundunar sojin ruwa mai amfani da makaman nukiliya
Shugaban Koriya ta Arewa ya ce birnin Pyongyang zai haɓaka rundunar sojin ruwan ƙasar zuwa wata runduna da ke da makaman nukiliya wadda za ta iya sarrafa tsarin yaƙin nukiliya yadda ya kamata a cikin yanayi na yaƙi.
Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin kafa rundunar sojin ruwa mai amfani da makaman nukiliya
Kim Jong-un ya yi alƙawarin gina rundunar sojin ruwa mai amfani da makaman nukiliya

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi alƙawarin kafa rundunar sojin ruwa wadda za ta riƙa amfani da makaman nukiliya, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na gwamnati suka ruwaito yayin da aka ƙaddamar da atisayen jiragen ruwa na ƙawayen Amurka.

Atisayen na wannan makon wanda ya haɗa Japan da Koriya ta Kudu da kuma Amurka an soma shi ne a shekarar 2023 a matsayin wani mataki ƙoƙarin hana barazanar makamai masu linzami da makaman nukiliya daga Pyongyang.

Kalaman Kim sun zo ne a yayin ƙaddamar da Kang Kon, wani jirgin ruwan yaƙi wanda ya nutse bayan ƙaddamar da aka shi a watan Mayun 2025, a birnin Wonsan mai tashar jiragen ruwa a ranar Lahadi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Koriya ya ruwaito.

"Ya kamata mu tabbatar da cewa an gudanar da ayyukan yaƙin nukiliya iri-iri cikin inganci don yaƙi na gaske ta hanyar haɓaka rundunar sojojin ruwanmu zuwa rundunar da ke amfani da makaman nukiliya," kamar yadda Kim ya shaida wa taron bikin na ranar Litinin.

"Da zarar an ƙaddamar da ita a kowane lokaci, sabuwar rundunar za ta mayar da hankali wajen kai munanan hare-hare kan maƙiya saboda ita ce rundunar da ke da hannu a cikin tsarin yaƙi da makaman nukiliya na ƙasa," in ji shi.

Hotunan da aka fitar na Kim sun nuna shi tare da 'yarsa, Ju Ae, wacce aka ce an naɗa ta a matsayin magajiyarsa.

A watan Yuli, Kim ya jagoranci gwajin Kang Kon, ɗaya daga cikin jiragen yaƙi guda biyu masu nauyin tan 5,000 da aka ƙaddamar a bara, bayan kwashe fiye da shekara da lalacewa a yayin bikin ƙaddamar da shi.

Bayanin Kim kan "rundunar ruwa mai ɗauke da makaman nukiliya" ya nuna cewa jiragen ruwan za su iya zama dandamalin harba makamai masu linzami masu ƙarfin nukiliya, in ji Lim Eul-chul, Farfesa a Jami'ar Kyungnam.

"Kai-tsaye kuma cikin zango"

Kim ya ƙara da cewa Koriya ta Arewa tana aiwatar da wani "muhimmin shiri" don ƙarfafa rundunar sojin ruwanta wanda za a nuna wa duniya "cikin watanni takwas".

Wannan zai iya nuna wata babbar kadara mai mahimmanci, kamar sabon jirgin ruwa mai ɗauke da makamai masu linzami masu harbi ta ƙarƙashin ruwa (SLBMs), in ji Lim.

Ta hanyar tura Kang Kon a Tekun Gabas, Pyongyang zai kuma nemi ci gaba da gudanar da atisayen haɗin gwiwa na teku da kuma tura kadarorin nukiliya "kai-tsaye kuma cikin zango", in ji Lim.

Ana sa ran atisayen ƙawancen Amurka na wannan makon, wanda aka yi wa laƙabi da Freedom Edge, zai gudana har zuwa ranar Jumma'a a yankin ruwan ƙasa da ƙasa a gabas da kudancin Tsibirin Jeju na Koriya ta Kudu.

An ci gaba da gudanar da atisayen ne duk da cewa Shugaba Donald Trump ya rage wasu atisayen ƙasarsa da Koriya ta Kudu, yayin da kuma yake shirin sake buɗe harkokin diflomasiyya da Pyongyang game da shirinta na nukiliya.

Koriya ta Arewa ba ta nuna wata alama ta mayar da martani ba.