| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Jihar Filato a Nijeriya ta rufe makarantu saboda ɓarkewar cutar mashaƙo
Matakin rufe makarantun ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa game da zargin barkewar cutar Mashaƙo a jihar.
Gwamnatin Jihar Filato a Nijeriya ta rufe makarantu saboda ɓarkewar cutar mashaƙo
Gwamnan Jihar Filato ta Nijeriya Caleb Manasseh Mutfwang

Gwamnatin Jihar Filato da ke arewacin Nijeriya ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu na wucin-gadi.

Hakan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a ƙarshen mako a matsayin wani mataki na kariya daga waɗanda ake zargi sun kamu da cutar mashaƙo (diphtheria).

Sanarwar wadda Kwamishinar Yada Labarai ta jihar, Joyce Ramnap ta fitar ta bayyana cewa, rufe makarantun zai soma aiki ne daga ranar Litinin, 7 ga watan Satumba har zuwa lokacin da gwamnati za ta sake fitar da “sanarwar buɗe makarantun.’’

"Umarnin na ɗaukar matakan kariya ne daga ɓarkewar cutar mashaƙo da ake zargi ta ɓarke a wasu sassan Jihar, musamman a ƙananan hukumomin Jos ta Arewa da Wase da Jos ta Kudu da kuma Bassa," in ji ta.

Kazalika Kwamishinar ta bayyana cewa rufe makarantun ya shafi dukkan makarantu, ciki har da waɗanda suka riga suka koma aiki a sabon zangon karatu na shekarar 2026 zuwa 2027.

"Saboda haka, an kuma umarci makarantun da suka soma karatu da su rufe daga ranar Litinin, kuma su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu sabuwar sanarwa," in ji ta.

Haka kuma an yi kira ga iyaye da malamai da kuma hukumomin makarantu da su bi wannan umarni da aka bayar.

Matakin rufe makarantun ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa game da fargabar ɓarkewar cutar mashaƙo a jihar.

Hukumomin lafiya a jihar Filato, sun tabbatar da cewa an samu rahoton ɓullar cutar a yankunan ƙananan hukumomi huɗu a cikin 'yan makonnin nan, wanda ya sa Ma'aikatar Lafiya ta “ɗauki matakan sa ido da mayar da martani kan al'ummomin da abin ya shafa.”

Cutar mashaƙo dai na yaɗuwa ne cikin sauri da ke shafar numfashi, musamman maƙogwaro da hanci, sannan ana kamuwa da ita ta hanyar iska da tari ko atishawa daga mai ɗauke da cutar.

A baya, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya NCDC ta shawarci jihohi da su ƙara himma wajen yin allurar rigakafi da wayar da kan jama'a da kuma gano waɗanda suka kamu da cutar da wuri don hana yaɗuwarta.