’Yanbindiga sun kashe mutane 10 tare da yin garkuwa da aƙalla wasu 40 daga wani ƙauye a arewa maso yammacin Nijeriya, a cewar wani rahoton tsaro da AFP ta gani ranar Litinin da kuma shaida da wani mazaunin yankin ya bayar.
Harin ya faru ne a garin Tofa, da ke Ƙaramar Hukumar Rabah a Jihar Sokoto, a cewar wani rahoto da aka shirya wa Majalisar Ɗinkin Duniya.
Hadiyyatullahi Hamisu, wani mazaunin Tofa, ya tabbatar da adadin waɗanda aka kashe da waɗanda aka yi garkuwa da su, inda ya ƙara da cewa maharan sun yi awon gaba da ɗumbin dabbobi.
Rahoton ya ɗora alhakin harin kan ’yanbindigar da ke biyayya ga Bello Turji, wani jagoran ’yanbindiga daga makwabciyar Jihar Zamfara.
Ƙaramar Hukumar Rabah tana iyaka da Jihar Zamfara, inda ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane da masu satar shanu ke gudanar da ayyukansu daga sansanonin da ke cikin dazuzzukan da suka ratsa jihohi da dama a arewa maso yamma da yankunan tsakiyar Nijeriya.
’Yansandan Sokoto ba su mayar da martani ga tambayar AFP kan lamarin ba.
Rahoton ya ce harin wani ɓangare ne na dabarun ’yanbindiga na amfani da garkuwa da mutane “a matsayin wata hanya mai ɗorewa ta samun kuɗaɗen shiga da kuma tashin hankalin kisa domin tsoratar da al’umma da ƙarfafa iko a yankunan da abin ya shafa.”
Ya kuma yi gargaɗin cewa lamarin na iya “kawo cikas ga ayyukan jinƙai” a yankin “saboda ƙarin haɗarin hare-hare.”
Arewa maso yammacin Nijeriya na ƙara fuskantar matsin lamba sakamakon ayyukan ’yanbindiga da kuma wasu ƙungiyoyin ’yanta’adda.
A watan da ya gabata, an kashe kusan Musulmai masu ibada 30 a lokacin da wasu da ake zargin ’yanta’adda ne suka kai hari garin Ungushi, da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe a Jihar Sokoto, yayin sallar Jumma’a, a cewar jami’an yankin.

















