| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Darakta Janar na DSS ya umarci jami'ansu da kar su kama kowa yayin da farar-hula suka samu sabani
Adeola Ajayi, darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ke Nijeriya ya umarci jami’ansu da kar su kama kowa idan aka samu sabani a tsakanin ‘yan kasar.
Darakta Janar na DSS ya umarci jami'ansu da kar su kama kowa yayin da farar-hula suka samu sabani
Tun bayan shigar sa ofis, shugaban hukumar DSS a Nijeriya na kawo sauye-sauye a ayyukan jami'ansu.

Adeola Ajayi, darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ke Nijeriya ya umarci jami’ansu da kar su kama kowa idan aka samu sabani a tsakanin ‘yan kasar.

Ajayi ya bayar da umarnin ne a lokacin wata hira da aka yi da wasu zababbun shugabannin kafofin watsa labarai a ranar Alhamis, yana mai cewa wani bangare ne na matakan karfafa bin doka da kuma inganta tarihin kare hakkin dan adam na hukumar.

Darakta Janar na DSS ya ce tun lokacin da ya hau kan mulki, ya gabatar da gyare-gyare a fannoni biyar, wadanda suka hada da jami'an tsaro, hadin gwiwa tsakanin hukumomi, sauke nauyi, girmama hakkin dan adam, da kuma gyare-gyaren kayayyakin more rayuwa da gudanarwa da nufin inganta gudanar da aikin.

A cewar sa, gyare-gyaren sun kuma fito da bambanci tsakanin batutuwan farar hula da na laifuka manya a cikin batutuwan da suka shafi hukumar, yana mai cewa kwarewarsa a aikin ya nuna cewa DSS ta cakuda bangarori biyun a baya.

Ya ce amfani da karfi bai dace ba a cikin takaddama tsakanin farar hula.

"Ba za ka iya amfani da amfani da karfi a cikin harkokin farar hula ba. Kuma ma wasu batutuwan laifuka ba sa bukatar karfi," in ji Ajayi.

Ya bayar da misali da karar da ta shafi Pat Utomi, masanin tattalin arziki na siyasa, kan zarge-zargen da suka shafi yunkurin kafa "haramtacciyar gwamnati".

"Maimakon kama shi, mun nemi fassara daga bangaren shari'a," in ji darakta janar din naDSS.

"Kuma kotun ta yanke hukuncin cewa abinda ya yi ya saba wa kundin tsarin mulki, haramtacciyar hanya ce, kuma barazana ce ga tsaron kasa."

Ajayi ya kuma tabo wani batu game da wata shari'a da ta shafi Kungiyar Shirin Haƙƙin Tattalin Arziki da Bin Dokoki (SERAP), yana mai cewa ƙungiyar ta je kotu kan zarge-zargen cewa jami'an DSS biyu sun kutsa kai harabarta.

Ya ce an bi diddigin lamarin a kotu ba tare da an kama kowa ba, ya ƙara da cewa daga ƙarshe kotun ta ba da fiye da Naira miliyan 100 ga jami'an DSS biyu bisa zargin ɓata suna, kodayake SERAP ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Ajayi ya ce yanzu DSS ta koma kotu kan al'amuran farar hula, ya ƙara da cewa ya umarci jami'an da kada su kama kowa a kowace shari'a ta farar hula.

Ya ce hukumar za ta kuma tuntuɓi kotu a shari'o'in da suka shafi 'yan jarida saboda "muna yin aiki ɗaya."

Ajayi ya bayyana 'yan jarida a matsayin "ƙwararrun abokan aiki" na DSS, yana mai cewa bambancin shi ne 'yan jarida suna sanar da jama'a yayin da DSS ke sanar da gwamnati.