| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Jiragen ruwa biyu na kasuwanci sun yi karo a gabar Tekun Silivri a Istanbul, mutum 10 sun ɓata
Hukumomin ruwan Turkiyya sun ce ana zargin jirgin da ya bace mai dauke da mutane 10 ya nutse ne bayan ya kasa amsa kiran da aka yi ta yi masa, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Jiragen ruwa biyu na kasuwanci sun yi karo a gabar Tekun Silivri a Istanbul, mutum 10 sun ɓata
Jirgin ruwan kasuwanci dauke da ma'aikata 10 ya nutse a gabar tekun Turkiyya - hukumomi

Jiragen ruwa biyu na kasuwanci dauke da tambarin tutar Turkiyya sun yi karo a gabar tekun gundumar Silivri da ke Istanbul da safiyar ranar Laraba, inda hukumomin ruwa suka ce ana zargin daya daga cikin jiragen ruwan ya nutse tare da ma’aikatansa 10 bayan da aka kasa samunsa a kiran da aka yi ta masa.

A cewar Ofishin Gwamnan Istanbul, Jirgin ruwan kasuwanci mai dauke da tambarin Turkiyya Alsu wanda ya taso daga Kocaeli zuwa Aliaga, ya yi karo da wani jirgin mai dauke da tambarin Turkiyya Tugberk Imamoglu da misalin karfe 3 na safe agogon yankin (0000GMT), wanda shi ma ya taso daga tashar jiragen ruwa ta Iskenderun zuwa Karadeniz Eregli.

Hatsarin ya auku ne daga nisan mil 18 na ruwan teku da ke kudu da gundumar Silivri.

Ofishin gwamnan ya ce an aika jiragen ruwa daga Babban ofishin Daraktan Tsaron Teku da Rundunar Tsaron Teku na Marmara da Tashoshin Jiragen Ruwa, tare da helikwafta na rundunar tsaron Teku, zuwa wurin da lamarin ya faru.

Binciken farko da tawagar binciken suka gudanar ya nuna cewa ba a samu wata barna sosai a jirgin Aslu ba.

A sanarwar da aka fitar, Ofishin babban Daraktan Hukumar Harkokin Ruwa ya ce ana zargin jirgin Tugberk Imamoglu ya nutse ne bayan kasa samunsa a kiran tarho kuma babu daya daga cikin ma'aikatan jirgin da ya amsa kiran wayoyinsu.

Hukumar ta ce ana ci gaba da kokarin aikin bincike da ceto yayin da hukumomi ke ci gaba da aiki don gano makomar ma'aikatan jirgin da suka bata.