Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya ta ce ta kwato bindigogi 676 na zamani da kuma harsasai fiye da 332,000, a wani ɓangare na ƙoƙarin da take yi na daƙile hanyoyin samar da makamai ga ‘yanta’adda da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a ƙasar.
Darakta Janar na DSS, Oluwatosin Ajayi, ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Trust, yayin da yake bikin cika shekara biyu da kama aiki a matsayin shugaban hukumar.
Ya ce an kwato makaman ne daga ranar 29 ga Mayun 2023 zuwa yanzu, kuma sun haɗa da nau’o’in bindigogi da harsasai daban-daban.
Ajayi ya ce ƙwace waɗannan makamai na daga cikin babbar dabarar hukumar ta hana makamai da harsasai isa hannun ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke da hannu a ayyukan ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka.
Ya bayyana cewa DSS ba ita kaɗai ke wannan aikin ba, inda ya ƙara da cewa sojoji, ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro su ma sun samu gagarumar nasara wajen ƙwato makamai. Sai dai ya jaddada cewa girman matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta na nufin hukumomin tsaro dole ne su ci gaba da ƙara ƙaimi.
Shugaban DSS ya ce akwai kuma buƙatar gwamnati ta ƙarfafa hukumomin tabbatar da doka tare da tabbatar da cewa masu aikata laifuka sun fuskanci hukuncin abin da suka aikata.
A cewarsa, kama waɗanda ake zargi da gurfanar da su a gaban kotu kaɗai bai isa ba; dole ne hukumomin tsaro su samar da ƙwararan hujjoji da za su kai ga samun hukunci a kotu.
Ya ce saboda haka DSS ta ƙara mai da hankali kan bincike, tattara shaidu da gurfanar da waɗanda ake zargi, yana mai cewa hukumar ta samu hukuncin kotu a wasu shari’o’in ta’addanci da sauran laifuka.
Ya ce DSS za ta ci gaba da ƙarfafa yaƙin da take yi da ta’addanci da aikata manyan laifuka, tare da inganta haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da kuma ƙara kusantar al’ummomi.
Ajayi ya ƙara da cewa ya kamata ‘yan Nijeriya su sa ran ƙara tsaurara matakan yaƙi da ‘yanta’adda da masu aikata laifuka, yayin da ya buƙaci ‘yan ƙasa su tallafa wa hukumomin tsaro maimakon samar wa masu laifi damar yin ayyukansu.
Ya jaddada cewa babban burin shi ne dawo da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar, yana mai cewa ƴan Nijeriya na matuƙar son ganin ƙarshen rashin tsaron da ya shafi al’ummomi tare da tarwatsa rayuwa da hanyoyin samun abin dogaro da kai.





















