Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress wato NDC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ba ta da ’yan takarar gwamna a jihohi 12, tana mai bayyana ikirarin a matsayin farfagandar ƙarya da aka shirya domin rage tasirin jam’iyyar da ke ƙara samun karɓuwa a fagen siyasa.
Jam’iyyar ta ce ta gabatar da ’yan takararta yadda ya kamata a zaɓen gwamna a dukkan jihohi 28 da za a gudanar da zaɓen a shekarar 2027.
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na NDC, Osa Director, ne ya bayyana matsayar jam’iyyar a cikin wata sanarwa, inda ya zargi waɗanda ke yaɗa rahoton da yin hakan da gangan domin yaudarar ’yan Najeriya game da shirin da jam’iyyar ta yi na tunkarar zaɓen.
Osa ya ce NDC ba jam’iyyar siyasa ce ta wani yanki kawai ba, illa dai wata ƙungiyar siyasa ce ta ƙasa baki ɗaya wadda ke da tsare-tsare, ’yan takara da magoya baya a dukkan jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya.
Domin karyata rahoton, jam’iyyar ta wallafa sunayen ’yan takararta a jihohi 12 da rahoton ya ambata a matsayin wuraren da ake zargin ba ta da ’yan takara.
Sun haɗa da Sanata Kabiru Marafa a Zamfara; Rear Admiral Ibrahim Sanusi Kasim (Mai Ritaya) a Borno; Hon. John Odey a Cross River; Babanta Michael Okon a Akwa Ibom; Nwofe Boniface a Ebonyi; da Yakubu Solomon Ndam a Filato.
Sauran sun haɗa da Ilu-Barde Aliyu a Katsina; Alhaji Umar Usman Besse a Kebbi; Jonga Yahaya Gabakau a Yobe; Dutse Aminu Sani a Jigawa; Farfesa Yahaya Mohammed Sani a Taraba; da Abdu Sidi Bomi a Neja.
Jam’iyyar ta ce ta fitar da jerin sunayen ne domin gyara bayanan da ba su dace ba da kuma mayar da martani ga abin da ta bayyana a matsayin yunƙurin da aka yi da gangan na nuna cewa ba ta shirya yadda ya kamata domin zaɓen 2027 ba.
Ta kuma yi kira ga ƙungiyoyin kafafen yaɗa labarai, ’yan jarida, masu rubutun ra’ayin kansu da masu ƙirƙirar abubuwan yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafa su, tana mai gargaɗin cewa yaɗa bayanan da ba a tantance ba na iya rage amincewar jama’a ga kafafen yaɗa labarai da kuma tsarin dimokuraɗiyya.
NDC ta ce za ta ci gaba da mayar da hankali kan siyasar da ta ginu kan manufofi da batutuwa, kuma ba za ta bari abin da ta bayyana a matsayin ƙaryace-ƙaryacen da aka ɗauki nauyin yaɗawa su ɗauke mata hankali daga manufofinta na siyasa ba.



























