| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Yawan iskar gas ɗin da Nijeriya ke samarwa a cikin gida ya ɗara ƙafa biliyan 2
Yawan iskar gas ɗin Nijeriya ke samarwa a yini a cikin ƙasar ya ɗara ƙafa biliyan biyu, yayin da gwamnatin ƙasar ke ƙoƙarin faɗaɗa samar da gas wa cibiyoyin samar da lantarki da masana'antu da kuma rage kalubale ga ci-gaban tattalin arziki.
Yawan iskar gas ɗin da Nijeriya ke samarwa a cikin gida ya ɗara ƙafa biliyan 2
Toshon Hoto: Baya ga matatar man Dangote, fannin makamashin Nijeriya na haɓaka

Adadin iskar gas ɗin da Nijeirya ke warewa ga kasuwar cikin gida ya ɗara ƙafa biliyan 2 a yini, yayin da ƙasar ke ƙoƙarin faɗaɗa samar da iskar gas ga tashoshin samar da lantarki da masana’antu da kuma rage tsaiko ga girman tattalin arziki, kamar yadda ministan man ƙasar ya bayyana ranar Jumma’a.

Yawan iskar gas da ƙasar ke samarwa ya tashi zuwa ƙafa biliyan 7.5 a yini daga kimanin ƙafa biliyan 6.8 a yini a shekarar 2023, kamar yadda ministan man fetur ɗin ƙasar Ekperikpe Ekpo ya bayyana. Adadin iskar gas ɗin da aka tabbatar cewa ƙasar na da shi a cikin ƙasa ya ƙaru zuwa ƙafa tiriliyan 215.19 daga ƙafa tiriliyan 208.83, in ji Ekpo.

Nijeriya na son iya samar da iskar gas ƙafa biliyan 10 a yini nan da shekarar 2027 da kuma ƙafa biliyan 12 nan da shekarar 2030 domin iya biyan ƙarin buƙatar da ake samu dagan ɓangarorin samar da makamashi da masana’antu da haɗa taki da masu sarrafa fetur da sinadirai da iskar gas samfurin NLG da sufuri da kuma kasuwannin ƙetare.

Domin taimaka wa samar da ƙarin iskar gas a cikin ƙasar, bututun iskar gas na Obiafu-Obrikom-Oben (OB3) ya kai ga kammalawa kuma ana shirya shi domin karɓar iskar gas ɗinsa na farko, in ji Ekpo. Bututun zai iya ɗaukar ƙafa biliyan biyu na iskar gas a yini kuma ana sa ran zai iya ba da damar ƙafa miliyan 500 na iskar gas ga kasuwar cikin ƙasar.

Zuba jari a fannin gas

Aikin bututun mai na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) ya kai kashi 95 cikin 100, in ji shi.

Ekpo ya ce naira biliyan 671 (dala miliyan $434 ) da aka fitar ta fannin dako da tace ɗanyen mai da rarraba tacaccen mai ya janyo kimanin naira tiriliyan 1.6 trillion (dala biliyan $1.2 ) a zuba jari na ‘yan kasuwa a faɗin ayyuka 31 da kuma ababen more rayuwa 205.

Ana tsammanin ayyukan su samar da kimanin iskar gas ƙafa miliyan 475 a yini a kasuwar cikin gidan ƙasar a lokacin da suka fara aiki. Nijeriya tana neman kimanin dala biliyan $30 na zuba jari a fannin gas nan da shekarar 2030.