Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta naɗa tsohon kocin tawagar Super Eagles Augustine Eguavoen a matsayin kocin wucin-gadi na tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Super Falcons gabanin wasan neman shiga gasar Olympic ta shekarar 2028.
Wata sanarwa da NFF ta fitar ranar Talata ta ce Eguavoen zai jagoranci tawagar ƙwallon mata ta ƙasa a zagaye na biyu na wasanni neman shiga gasar Olympic inda za su kara da Comoros a watan Oktoba, yayin da ake ci gaba da neman sabon koci na dindindin.
Hukumar NFF ta ce Eguavoen, wanda aka fi sani da suna “Cerezo”, ya zo aikin ne da ƙwarewa, bayan ya jagoranci tawaga a mataki mafi ƙololuwa a ƙwallon ƙafa.
Sanarwar ta tuno da cewa ya taɓa kasancewa kocin tawagar Super Eagles inda ta samu lambar yabo ta tagulla a gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2006 a Masar.

Eguavoen zai samu taimakon Christopher Danjuma, kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa da ke lig ɗin mata ta Nijeriya ta Nasarawa Amazons. Danjuma ya daɗe yana aiki da tawagogin mata na ƙwallon ƙafa ta Nijeriya kuma ya jagoranci Falconets a gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan ƙasa da shekaru 20 da a aka yi a shekarar 2024 a ƙasar Costa Rica.
Tsohon mai horas da golan tawagar Super Eagles Olatunji Baruwa zai kasance mai horas da gola. Ya yi aiki a baya da tawagogin ƙwallon ƙafa na Nijeriya, ciki har da Super Eagles da CHAN Eagles da Flying Eagles da Golden Eaglets.
Tsohon ‘yarwasan bayan Super Falcons kuma kociya Ayisat Yusuf za ta kasance cikin jami’an horaswar a matsayin mataimakiyar koci.
Yusuf ta buga wasanni 68 wa Nijeriya kuma ta wakilci ƙasar a gasar kofin Afirka sau huɗu da gasar kofin duniya sau uku da wasannin Olympic na shekarar 2008 da aka yi a Beijing.
Tawagar wadda ta kasance zakarar Afirka sau 10 za ta fara ƙoƙarin shiga wasannin Olympic da karawa na zagaye na biyu da Comoros, inda za su yi wasanni biyu a filin wasan Remo Stars da ke Ikenne-Remo ranar 9 da ranar 13 ga watan Oktoba na shekarar 2026.
Tawagar Super Falcons ta samu damar shiga zagaye na biyu a matsayin ɗaya daga cikin tawagogi da suka fi matsayi a gasar neman shiga wasannin, yayin da Comoros ta yi gaba bayan ta doke Sudan da ci 30-0.
Dole Nijeriya ta bi ta zagaye huɗu na wasannin sile-ɗaya-ƙwale bibbiyu domin samun ɗaya daga cikin gurabe biyu na Afirka a wasannin Olympic da za a buga a Los Angeles a shekarar 2028.
Idan ta samu ta doke Comoros, Super Falcons za ta wuce zagaye na uku, wanda za a buga ranar 23 ga watan Fabrairu da ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2027, inda za su haɗu da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ko kuma Maroko.


















