Shugaba Bola Tinubu ya nemi a bai wa Afirka kujeru na dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), da ikon hawa kujerar-na-ƙi, yana mai cewa tsarin da ake kai a yanzu yana cike da rashin adalci.
Tinubu ya gabatar da buƙatar ce ranar Alhamis a jawabin da ya gabatar ga muhawarar Babban Zauren MƊD na 81 a New York na Amurka.
Jawabin na shugaban, wanda Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya gabatar, ya kuma yi kira da a ware kujeru biyar na wucin-gadi ga nahiyar Afirka a Kwamitin Tsaron.
Ya ce dole a fara gyaran MƊD ne da sake tsarin Kwamitin Tsaron, yana mai cewa Afirka ba za ta iya ci gaba da ba da gudunmawa ga ajandar kwamitin, ba tare da wakilci na dindindin ba.
“Gyara wannan hukumar dole ya ya fara ne da sake tsara Kwamitin Tsaro, domin duniyar shekarar 2026 ba za ta iya kasancewa a ƙarƙashin ikon tsarin rarraba iko na shekarar 1945 ba. Afirka ba za ta iya ci gaba da cike ajandar kwamitin ba yayin da babu ita a cikin masu kujerun dindindin na kwamitin.
Nijeriya tana buƙata, bisa yarjejeniyar Ezulwini da kuma Alƙawarin Sirte, aƙalla kujerun dindindin biyu ga Afirka, da dukkan ‘yanci da nauyi na kujerar dindindin ciki har da ikon hawa kujerar-na-ƙi har zuwa iya ƙarshen rayuwar kwamitin, da kuma kujeru biyar na wucin-gadi gaba ɗaya. Ikon iya magana a madadin bil’adama na da nauyin wakiltarsa.”
Tinubu ya ce Nijeriya ta shirya domin ɗaukar ƙarin nauyi a fannin zaman lafiya da tsaro na ƙasa da ƙasa, inda ya yi ishara ga gudunmawar ƙasar ga kiyaye zaman lafiya da kuma shiga tsakani a faɗin Afirka.
Ya zayyano ayyukan shiga tsakanin da Nijeriya ta yi a Laberiya da Saliyo da Darfur da Mali da kuma Gambiya, yana mai ƙarawa da cewa ƙasar ta ci gaba da inganta shiga tsakani da tsarin Dimokuraɗiyya da tsaron lafiya ta ƙungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka da kuma haɗin gwiwa na yankin Gulf na Guinea.


















