| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Mutane da dama sun mutu yayin da wasu ke asibiti bayan sun sha wani maganin gargajiya a jihar Ondo
Ma’aikatar Lafiya ta jihar Ondo ta ce sakamakon binciken farko ya nuna yiwuwar mace-macen da alaka da shan wasu magungunan gargajiya da giya da ake hada su a gida.
Mutane da dama sun mutu yayin da wasu ke asibiti bayan sun sha wani maganin gargajiya a jihar Ondo
Mutane da dama sun mutu yayin da wasu ke asibiti bayan sun sha wasu maganin gargajiya a jihar Ondo

Akalla mutane 24 ne suka mutu, yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti bayan sun sha wani maganin gargajiya da giya da ake zargin sun gurbata a wasu sassan jihar Ondo da ke yankin kudu maso yammacin Nijeriya.

An samu rahoton mace-macen ne a ƙarshen makon da ya wuce a garuruwan Araromi Obu da Odigbo, da ke karamar hukumar Odigbo.

Rahotanni sun ce mutane takwas sun mutu a Araromi Obu, yayin da wasu 16 suka mutu a Odigbo.

Wasu mazauna yankin sun ce wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun mutu ne a gidajensu, ciki har da wadanda suka mutu yayin da suke barci.

Lamarin ya janyo zanga-zangar matasa a Araromi Obu, inda suka je fadar mai martaba Oba Rufus Akinrinmade domin neman a dauki matakin gaggawa.

Ma’aikatar Lafiya ta jihar Ondo ta ce sakamakon binciken farko ya nuna yiwuwar mace-macen da alaka da shan maganin maganin gargajiya da giya da ake hada su a gida.

Babban Sakataren ma’aikatar, Ayodele Adiji, ya ce ana ci gaba da gwajin samfuran da aka dauka domin gano ko magungunan gargajiyar ne suka haddasa mace-macen.

Kazalika Shugaban karamar hukumar Odigbo, Taiwo Adegoroye, ya sanya dokar hana sayarwa da kuma shan wasu magungunan gargajiya na tsawon wata guda a matsayin matakin kariya.

Binciken farko da jami’an lafiya na karamar hukumar suka yi ya nuna yiwuwar alakarsu da lamarin, a cewar Kwamishinan Lafiya na jihar, Banji Ajaka, yana mai kari da cewa gwamnati na ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa mace-macen.

Ya kuma bukaci jama’a da su guji yada bayanan da ba a tabbatar da su ba ko kuma danganta mace-macen da wani takamaiman abu kafin hukumomi su kammala bincike.